BindiddigiShin London Clinic da Buhari ya rasu karamin asibiti...

Shin London Clinic da Buhari ya rasu karamin asibiti ne?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Binciken Alkalanci ya tabbatar da cewa mashahuran shugabannin duniya sun kwanta a asibitin London Clinic kuma asibiti ne mai zaman kansa da yake kan gaba waje kwarewa a kaf kasar Burtaniya. Asibitin na da kwararrun likitoci surgeons da kwararrun masana lafiya sama da dari bakwai da kuma masu kula da lafiya da ma’aikata 1,300. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa asibitin karami ne karya ne.
Asibitin London clinic da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu dai asibiti ne dake kasar Burtaniya.
Wasu mutane a Najeriya saboda da sunji ance “Clinic” na maganar cewa Buhari ya mutu a wani karamin asibiti a Landan.
Akwai wani malamin addinin musulunci a Jos da ya yayi ikirarin cewa asibiti karami ne matuka.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci tayi bincike kan shin karamin asibiti ne kamar yadda ake fada ko yaya?
Yaushe aka bude asibitin?
Asibitin London Clinic dai an bude shi a shekarar 1932 wato ya zuwa yanzu ya kusa shekaru dari da kafuwa.
Inda asibitin yake
Da farko dai asibitin mai suna London Clinic na babban gininsa a gini mai lamba 20 Devonshire Place London W1G 6BW.
Hoton babban ginin asibitin London Clinic
Sannan akwai wani reshe da suke kira  The Duchess of Devonshire wing dake gini mai lamba 22 Devonshire Place London W1G 6JA. Sauraniyar Ingila Queen Elizabeth ta biyu ita ce ta bude wannan reshe a shekarar 2010.
Wani rashen asibitin London Clinic
Dakunan ganin likita ko duba marasa lafiya na asibiti London Clinic su kuma suna gini mai lamba 5 Devonshire Place London W1G 6HL.
Wani reshen na asibitin London clinic

Akwai wasu dakunan ganin likita dake gini mai lamba

 116 Harley Street London W1G 7JL.
Sanannun mutane da suka taba kwanciya a asibitin
Akwai manyan shugabannin duniya da suka taba kwanciya a wannan asibiti na London Clinic.
Misali a shekarar 2024 Sarkin Ingila Charles ya kwanta a wannan asibiti na London Clinic, don masa aiki kan kansar mafitsara.
‘Yarsa Law Ket itama a wannan shekarar ta kwanta a wannan asibiti na London clinic.
Tsohon shugab kasar Amurka John Kennedy shima ya taba kwanciya a wannan asibiti na London clinic.
Yawan ma’aikatan da kudin gudanar da asibitin

A rahoton asibitin na shekarar 2023, asibitin na da kwararrun likitoci da ake kira surgeons da kwararrun masana lafiya 750. Haka zalika akwai sauran ma’aikatan lafiya da ma’aikatan asibitin da suka kai 1,300.

Hoton rahoton asibitin na shekarar 2023
Asibitin London Clinic dai anyi ittifakin cewa yana cikin na daya zuwa na uku na asibitoci masu zaman kansu da suka fi iya aiki da kwarewa a kaf Burtaniya.
Asibitin London Clinin na kashe kudin daya kai Pound  miliyan casa’in da daya (£91m) wato sama da Naira biliyan dari da tamanin da shida (N186,498,403,000)
wajen biyan ma’aikatan sa a shekara. Yana kuma kashe Pound miliyan dari da saba’in da uku (£173m) wato sama da Naira biliyan dari uku (N354,586,163,000).
wajen gudanar da asibitin.
Asibiti har ila yau yana kashe kudin daya kai pound miliyan goma sha daya (£11m) wajen bada tallafi wato Charity.
Sakamakon bincike:
Binciken Alkalanci ya tabbatar da cewa mashahuran shugabannin duniya sun kwanta a asibitin London Clinic kuma asibiti ne mai zaman kansa da yake kan gaba waje kwarewa a kaf kasar Burtaniya. Asibitin na da kwararrun likitoci surgeons da kwararrun masana lafiya sama da dari  bakwai da kuma masu kula da lafiya da ma’aikata 1,300. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa asibitin karami ne karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar