BindiddigiIna Gaskiyar Harin Kunar Bakin Wake A CBN?

Ina Gaskiyar Harin Kunar Bakin Wake A CBN?

-

An dai cigaba da samun kirkirarrun hotuna da ake amfani da fasahar AI (deep fake) dake yaduwa tare da yadasu domin kawar da kan mutane ko yada labarun karya.

Batu:

Wani shafin Facebook mai suna Wakiliya ya wallafa wasu hutuna guda biyu ranar 26/12/2024 tare da ikirarin cewa “ YANZU YANZU: An kai harin kunar bakin wake a babban bankin Najeriya da ke Abuja, inda ake fargabar mutuw@ mutane da dam@ tare da lalata dala biliyan 100.
Wani dan kun@r bakin w@ke ya lalat@ babban bankin Najeriya gaba daya a ranar Kirsimeti – abin da ke faruwa a yanzu.”
Wannan wallafa dai ta sami tofa albarkacin baki sama da dari da talatin da kuma shares sama da dari da tamanin.((https://www.facebook.com/share/p/1XUnJYWxFx/?))

Bincike:

Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta fara karanta ikirarin inda ikirarin ya nuna cewa harin bam din ya faru ranar kirsimeti wato ranar 25/12/2024 wato awanni ashirin da hudu kafin a wallafa ikirarin da hotunan.
Sannan kafar bindiddigi ta Alkalanci ta duba duk kafafen yada labarai don ganin ko an wallafa wannan irin babban labari na hari a babban bankin Najeriya CBN to amma babu ko daya.
Alkalanci ta sanya hoton farko a wata manhajar duba hotuna inda ta tabbatar da cewa tsarin ginin na babban bankin Najeriya ne to amma anyi amfani da kirkirarriyar basira ta AI wajen sanya alamun rushewar da ake gani a hoton.
Hoto na biyu ma manhajar ta nuna kamanceceniya da wani ofishi a kasar Bangladesh da aka tarwatsa abubuwa wanda shima anyi amfani da kirkirarriyar fasaha ta AI wajen samar dashi.
Haka zalika kafar Alkalanci ta tuntubi wani ma’aikacin babban bankin na Najeriya a Abuja wanda yace wannan labarin karya ne.

Sakamakon Bincike:

Bisa la’akari da rashin daidaiton ikirari a rubutun, dama hotunan da kuma rashin samun wannan babban labari a sahihan gidajen jaridu yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Ina gaskiyar cewa Amurka, Faransa ke neman haddasa faɗa tsakanin Sudan da Chadi?

  Duk lokacin da aka sami wata hatsaniya ko rikici tsakanin kasashe, wasu na amfani da wannan dama wajen yada...

Bidiyon ƴan sanda sunyi kame a Edo ƙarya ne, bidiyon ya faru a Ghana ne

  A yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da Allah wadai da kisan wasu matafiya a jihar Edo, wasu na...

Karanta wannan

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar