BindiddigiShin Akwai Sansanin Sojan Faransa A jihar Borno?

Shin Akwai Sansanin Sojan Faransa A jihar Borno?

-

Gwamnatin kasar Nijar dai na cigaba da zargin gwamnatin Najeriya wajen cewa tana hada kai da kasar Faransa domin tada hargitsi a kasar ta Nijar. Wadannan zarge-zarge dai na zuwa da ikirarin karya.

Batu:

Akwai wani bidiyo dake yaduwa a kafofin sada zumunta da dama dake nuna shugaban mulkin soji na kasar Nijar yana hira da wani dan jarida inda a ciki yayi ikirarin cewa;
Shugaban Najeriya ya amshi kudi daga Faransa domin basu guri a Borno inda suka kafa wani sansanin soji gurin da suke kira “Canada”.

Bincike:

Binciken da kafar bindiddigi ta  Alkalanci  tayi tun kwanakin baya ya tabbatar da cewa babu sojin Faransa a jihar Borno balle ma kafa sansani.
Sabon bincike bayan wannan bidiyo wanda ya hada da tuntubar dakarun sojin Najeriya dake aiki a jihar Borno ya tabbatarwa da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci cewa babu wani sojin Faransa dake yankunan Kurnawa, Kangarwa da Dogon Chikun da shugaban na Nijar yayi ikirari a bidiyon. Domin kuwa yanki ne da ‘yan kungiyar ISWAP ke kai farmaki sosai.
A kwanakin baya ma dai shalkwatar tsaron Najeriya ta musunta shirin kafa sansanin sojin wata kasa a Najeriya wanda aka dinga yada tsohon bidiyo sojin Birtaniya a matsayin sojin Faransa.
Mai magana da yawun ministan harkokin wajen Najeriya Alkasim Abdulkadir shima ya musunta samar da sansanin sojin Faransa mai suna CANADA a jihar ta Borno. “Tabbas shugaba Tinubu yaje Faransa wanda kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi irin lafiya, sanya hannun jari, sufuri, noma da lantarki haka  kuma akwai ‘yan kasuwar Najeriya da suma suka sanya hannu domin fara bude kasuwancin su a Faransa . Najeriya kasace mai tasowa kuma ta sanya irin wannan yarjejeniya da kasashe irin su China, America, Rasha da Japan.
Ofishin jakadancin Faransa a Najeriya shima ya musunta shirin samar da sansanin soji a Najeriya.

Sakamakon bincike:

Bisa kasa samun wata hujja ta wanzuwar ko samuwar sansanin soji balle sojin wata kasa a yankin da shugaban na Nijar ya ambata yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar