Dokokin ƙasar Nijar ga kafafen yaɗa labarai nada tsauri inda kafafen na gwamnati dama masu zaman kansu basa sanya waƙoƙin siyasa irin na Rarara.
Batu:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani rubutu (archived here) ranar 1/1/2025 inda yake cewa “An haramta sauraron waƙoƙin Rarara a Niger”
Wannan wallafa ta sami tofa albarkacin baki wato comments sama da dari tara yayin haɗa wannan bincike.

Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta tuntubi wani babban dan jarida dake babban birnin ƙasar ta Nijar Yamai mai suna Yusuf Abdoulaye inda ya bayyanawa Alkalanci cewa babu wata sanarwa makamanciyar hakan daga hukumomi.
“Dama mu anan Nijar ba’a sanya waƙoƙin irin na Rarara a gidajen Rediyo domin dokokin gidajen yaɗa labarai nada tsauri. Tabbas akwai labarai dake yaɗuwa cewa Rarara yace zai yiwa Shugaba Tchiani waƙa ta ɓatanci. A hukumance gaskiya babu wancan labari kuma na tuntubi wasu jami’an gwamnati sunce ya zuwa yanzu (2/1/2025) babu wata sanarwa makamanciyar hakan.“
Sannan kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi wani mamallakin gidan Radiyo a jihar Maraɗi Mansour Sani wanda yace ya zuwa ranar 2/1/2025 babu wata sanarwa a hukumance na wannan iƙirari zuwa ga gidajen Radiyo koma al’ummar gari, dama mu a gidajen Radiyo bama sanya waƙoƙin Rarara saboda na siyasa ne inji Mansour.
Tun bayan juyin mulkin soji a ƙasar ta Nijar dai babu ma’aikatar yaɗa labaru.
Sakamakon bincike:
Bisa la’akari da kasa samun wannan labari daga jami’an gwamnatin Nijar, sahihan gidajen jaridu da ƴan jaridun ƙasar, yasa kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan iƙirari ƙarya ne.