BindiddigiNishadiIna Gaskiyar Wakar Naziru Ta Zagin Rarara?

Ina Gaskiyar Wakar Naziru Ta Zagin Rarara?

-

Makawakin siyasa a Najeriya Rarara ya kasance mutumin da ake ta ambata a shafukan sada zumunta  tun bayan hirarsa da kafar DCL Hausa inda yayi magana kan rikicin shugabanin Najeriya da Nijar.

Batu:

Wani shafin Tiktok mai suna @abdou.salam.absi2 ya wallafa wani faifan bidiyo a ranar 5/1/2025 inda akaga mawakin nan Naziru sarkin waka kuma aka rubuta “New song by sarkin waka 🎶”
Hoton bidiyon dake cigaba da yaduwa.
Hoton bidiyon dake cigaba da yaduwa.
Wani shafin na Tiktok mai suna @binta56905 ya wallafa wannan (archived here) waka da bidiyo a ranar ta 5/1/2025.
Hoton bidiyon dake cigaba da yaduwa.
Hoton bidiyon dake cigaba da yaduwa.

Bincike:

Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi wani dan jarida dake aiki da gidan Talabijin na Arewa24 wanda ke gabatar da shirin fitattun wakoki Abubakar Habib Ibrahim inda yace; “ wannan ba Naziru Sarkin waka bane, domin duk da muryar ta danyi kama amma ba shi bane. Idan ka kula da kyau yanayin bakin Nazirun a wannan bidiyo bai hau wakar ba.”
Sannan kafar Alkalanci ta duba shafin Tiktok da Instagram na Naziru Sarkin waka amma bata sami wannan bidiyo ko wakar ba.

Sakamakon Bincike: 

Bisa kasa samun wakar a shafukan Naziru Sarkin waka da kuma bayanin dan jarida mai gabatar da shiri dangane da wakoki Abubakar Habib Ibrahim yasa kafar bindiddigi ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa wannan iƙirari ƙarya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar