BindiddigiShin An Haramta Jin Waƙoƙin Rarara A Nijar?

Shin An Haramta Jin Waƙoƙin Rarara A Nijar?

-

Dokokin ƙasar Nijar ga kafafen yaɗa labarai nada tsauri inda kafafen na gwamnati dama masu zaman kansu basa sanya waƙoƙin siyasa irin na Rarara.

Batu:

Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani rubutu (archived here) ranar 1/1/2025 inda yake cewa “An haramta sauraron waƙoƙin Rarara a Niger”
Wannan wallafa ta sami tofa albarkacin baki wato comments sama da dari tara yayin haɗa wannan bincike.
Hoton Ikirarin Dake Cigaba Da Yaduwa.
Hoton Ikirarin Dake Cigaba Da Yaduwa.

Bincike:

Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta tuntubi wani babban dan jarida dake babban birnin ƙasar ta Nijar Yamai mai suna Yusuf Abdoulaye inda ya bayyanawa Alkalanci cewa babu wata sanarwa makamanciyar hakan daga hukumomi.
Dama mu anan Nijar ba’a sanya waƙoƙin irin na Rarara a gidajen Rediyo domin dokokin gidajen yaɗa labarai nada tsauri. Tabbas akwai labarai dake yaɗuwa cewa Rarara yace zai yiwa Shugaba Tchiani waƙa ta ɓatanci. A hukumance gaskiya babu wancan labari kuma na tuntubi wasu jami’an gwamnati sunce ya zuwa yanzu (2/1/2025) babu wata sanarwa makamanciyar hakan.
Sannan kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi wani mamallakin gidan Radiyo a jihar Maraɗi Mansour Sani wanda yace ya zuwa ranar 2/1/2025 babu wata sanarwa a hukumance na wannan iƙirari zuwa ga gidajen Radiyo koma al’ummar gari, dama mu a gidajen Radiyo bama sanya waƙoƙin Rarara saboda na siyasa ne inji Mansour.
Tun bayan juyin mulkin soji a ƙasar ta Nijar dai babu ma’aikatar yaɗa labaru.

Sakamakon bincike:

Bisa la’akari da kasa samun wannan labari daga jami’an gwamnatin Nijar, sahihan gidajen jaridu da ƴan jaridun ƙasar, yasa kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan iƙirari ƙarya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar