BindiddigiKo Majalisar Dinkin Duniya Na Neman Masu Fassara A...

Ko Majalisar Dinkin Duniya Na Neman Masu Fassara A Jihohin Arewacin Najeriya?

-

Yaren Hausa dai na cikin yarukan dake kara samun tagomashi a kasashen duniya dama kungiyoyin kasa-da-kasa domin kokarin isar da sako ga miliyoyin masu magana da Yaren a yammaci da tsakiyar Afrika.

Batu:

A ‘yan satittikan da suka gabata dama zuwa yanzu an sami mutane da dama dake yada wani rubutu da aka wallafa dake dauke da hoton hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya UNHRC inda sanarwar ke cewa UN na neman masu fassara daga wasu jihohin arewacin Najeriya.
An dai ta yada wannan rubutu a WhatsApp dama sauran kafofin sada zumunta wanda ya hada da Facebook.
Misali akwai wani mai suna Muhammad Nafiu wanda ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na Facebook.
Akwai wani shafi mai suna www.ngojobsite.com ya wallafa wannan sanarwa a ranar 14 ga watan Oktaban 2024 na bukatar masu fassara.
Jihohin da sanarwar tace ana neman masu Fassarar sun hada da Adamawa, Borno, Gombe, Jagawa, Kaduna, Kano, sauran sune Katsina, Kebbi, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara.
A karshen sakon dake wannan shafi ya nuna cewa duk wanda yake da sha’awar aikin zai tura sakon e-mail zuwa ga wani e-mail da aka rubuta kamar haka (Interested and qualified candidates should send their Applications to: [email protected] using the job title as the subject of the mail.)

Bincike:

Alkalanci ta tuntubi maimagana da yawun hukumar ta UNHCR a Najeriya Gabriel Adeyemi inda ya bayyana cewa “Banga wannan sanarwa ba kuma banda labarinta, ina mai tabbatar maka duk sanarwa musamman ta daukar aiki indai baya shafin hukumar to karya ne.”
Sannan mun tuntubi mani jami’i a ofishin majalisar dinkin duniya shima ya yace baida masaniya dangane da batun daukar masu fassara tare da karin cewa UN na wallafa bukatar daukar ma’aikata a shafinta dama jaridu Idan bukatar hakan ta taso.

 

Sakamakon bincike:

Bisa bayanan mai magana da yawun hukumar ta UNHCR a Najeriya dama duba shafin UNHCR da UN, haka zalika da bayanin wani ma’aikacin ofishin majalisar dinkin duniya a Najeriya da Alkalanci ya tattaro ya tabbatar da cewa wannan sanarwa karya ce wato false a turance.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar