Tun bayan juyin mulki da akayi a kasar Nijar dai ake ta samun tataburza tsakanin kasar Faransa da Nijar wanda hakan ya haddasa yaduwar labarun karya.
Batu:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani ikirari (archived here) ranar 22/12/2024 cewa “ 🛑Faransa ta maka Nijar kara kotun duniya saboda Uranium” wannan wallafa dai ta sami tofa albarkacin baki wato comments 350 da kuma shares 71, Sai kuma likes sama da dubu daya yayin wannan bincike.
Bincike:
Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta fara da bincikar batun alakar Faransa da Nijar kan Uranium inda ta gano cewa batun haka ko fitar da uranium daga Nijar ba gwamnatin Faransa bace face kamfani mai zaman kansa na Orano wanda yake amfani da wani kamfanin dake karkashin sa (subsidiary) mai suna Imouraren. Kasar ta Faransa dai nada hannun jari a kamfanin.
Sannan binciken kafar bindiddigi ta Alkalanci ta gano cewa kamfanin na Orano ya kai gwamnatin kasar ta Nijar sashen sulhu na kasa da kasa kan kwace lasisin aiki da kasa ta Nijar tayi.
Haka zalika da kafar bindiddigi ta Alkalanci y’a tuntubi ofishin jakadanci Faransa a Najeriya ya turowa da amsar cewa gwamnatin kasar Faransa bata kai Nijar kotu ba face kamfanin Orano ne ya kai kasar ta Nijar sashen sulhu wato arbitration a turance domin batun soke lasisin kamfanin dake karkarshin sa da gwamnatin Nijar tayi.
Sakamakon Bincike:
Bisa bayanan da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta samu na tabbatar da cewa sashen sulhu aka kai kasar Nijar kuma ba gwamnatin kasar Faransa bace wato kamfanini Orano ne. Sannan kotun duniya na duba batun laifukan yaki da wasu batutuwa na kasa da kasa wanda yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.