BindiddigiShin Bakanuwa Ce Ta Farko Data Zama Kwamishinan ‘Yan...

Shin Bakanuwa Ce Ta Farko Data Zama Kwamishinan ‘Yan Sanda A Arewa?

-

Nuna wane ko wance sune na farko da suka zama ko suka kware kan wasu ayyuka ko fannoni na zuwa da ikiraran karya a yawancin lokuta.

Batu:

Wani shafin Tiktok mai suna TrustRadioLive da shafin Facebook irin wannan suna sak Trust Radio Live ya wallafa wani hoto tare da rubuta a ranar 30/12/2024 dake cewa; “Bakanuwa ta zama ‘yar Arewa ta farko data zama kwamishinan ‘yan sanda”

Baya ga hoton dake dauke da wannan rubutu da kuma hoton ita kanta wacce ake magana akai anyi rubutu mai tsayi inda a sakin layi na farko aka rubuta cewa “ ’Yar Jihar Kano, Hauwa Ibrahim Jibrin, ta kafa tarihin samum ƙarin girma zuwa muƙamin Kwamishinan ’Yan Sanda, wanda ba a taba samun ’yar Arewa da ta kai wannan matsayi ba a tarihin Najeriya.”
Hoton wallafar shafin Tiktok mai suna TrustRadioLive.
Hoton wallafar shafin Tiktok mai suna TrustRadioLive.
Hoton wallafar shafin Facebook mai suna Trust Radio Live.
Hoton wallafar shafin Facebook mai suna Trust Radio Live.
Wani shafi mai suna Uzairu Lawal Rigasa shima ya wallafa irin wannan ikirari a ranar 30/12/2024 inda yace “ Bakanuwa ta zama ’Yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’Yan sanda”

Bincike:

Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa kafin Hauwa Ibrahim Jibrin ta zama kwamishinan ‘yan sanda a shekarar 2024 an sami mace ‘yar arewa daga jihar Benue mai suna Farida Waziri wacce ta zama kwamishina ta zama mataimakiyar sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya AIG wanda kuma ta zama Shugabar hukumar EFCC.
Hoton Farida Waziri da mukamin AIG.
Hoton Farida Waziri da mukamin AIG.
Haka zalika binciken Alkalanci ya gano wata ‘yar arewa da aka haifa a jihar Adamawa kuma mata ga wani Basarake a jihar Taraba mai suna Aisha Abubakar Abdulwahab wacce ta zama kwamishinan ‘yan sanda a shakarar 2016 kuma ta sami karin girma zuwa mukamin mataimakiyar sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya AIG.
Hoton AIG Aisha Abubakar.
Hoton AIG Aisha Abubakar.

Sakamakon bincike:

Bisa samo mata biyu ‘yan Arewacin Najeriya daya daga Arewa maso gabas daya daga Arewa maso tsakiya da suka taba zama kwamishinan ‘yan sanda dama haurawa zuwa mukamin maitaimakin sufeta Janar AIG yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirarin karya ne.
Karin bayani: TrustRadioLive ya goge wallafar na shafin Tiktok tare da gyara wallafar shafin Facebook.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar