Tun bayan juyin mulkin da sojojin Nijar sukayi dai an sami takun saka tsakanin kasar ta Nijar da kasashen duniya dama kungiyoyin irin su ECOWAS wanda ya haddasa aka sanyawa kasar takunkumi. Hakan dai ya janyo samun labarai da ikirari kala-kala da suke ba gaskiya ba ko wadanda akayi don sauya tunanin mutane.
Batu:
Akwai wani matashi da ya wallafa wani bidiyo mai tsawon mintuna biyu da sakan ashirin da takwas a kafar sada zumunta ta Tiktok mai suna @habib_niger_fillengue (Adana bayanai a NAN) inda yake ikirarin cewa za’a samar da sansanin soja na hadaka tsakanin Najeriya da kasar Faransa. A cikin bidiyon dai akwai ikirari da yawa da suka hada da cewa;
Babu alaka tsakanin Najeriya da Nijar a hukumance.
Ana shirin sanya sansanin sojan Faransa a iyakar Najeriya da Nijar.
Najeriya na dakile cigaban Nijar.
Wadannan dai na cikin manyan Ikirarin da yayi a wancan bidiyo.
“Wannan kira ne ga ‘yan uwana yan Nijar game da base militee da za’a dora a iyakar Najeriya da Nijar. Abinda ya kamata ‘yan Nijar ku sani fa Najeriya a hukamance basu da alaka damu (Nijar) a gwamnatance kenan tunba yanzu ba. Najeriya na alaka ne don talakawa mu Muna alaka da juna, amma a hakumance mun dade bama alaka dasu. Najeriya zata iya alaka da kowacce kasa a duniya domin kasa ce mai zaman kanta, haka Nijar zata iya alaka da kowacce kasa domin kasa ce mai zaman kanta…”
Hoton bidiyo da aka wallafa dake cigaba da yaduwa
Bincike:
Kafar bin diddigi ta Alkalanci ta fara da binciken shin akwai alaka tsakanin Najeriya da Nijar a hukumance ko babu?
Mai magana da yawun ministan harkokin kasashen waje ta Najeriya Alkasim Abdulqadir ya fadawa Alkalanci cewa tun samun ‘yancin kai Najeriya ke da alaka mai kyau tsakaninta da Nijar a hukumance. Ya kara da cewa “Shugaban Najeriya Bola Tinubu bayan hawa karagar mulki ya dawo da dukkan jakadun Najeriya a duk kasashen duniya amma ya bar na kasar Nijar Ambasada Mohammed Sani Usman domin nuna muhimmanci da kuma tabbatuwar alaka tsakanin kasashen biyu a hukumance.” Ya kara da cewa; “ko a watan satumbar daya gabata ai hafsan hafsoshin Najeriya Janar Christopher Musa ya kai ziyara inda ya gana da takwaransa na Nijar kan batun alakar dake tsakanin kasashen a fannin tsaro wanda yake a hukumance. Domin kasashen biyu na cikin gamayyar dakarun tsaro na MJTF dake yaki da ‘yan ta’adda.”
Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta tattauna da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijar Amadou Ango Souley ((Responsable de la communication du Ministère des Affaires Étrangères auprès du Ministre)) inda yace wannan ikirari karyane. “Inda babu alaka tsakanin Najeriya da Nijar jakadan Najeriya ya zauna a nan Nijar? Shima jakadan Nijar ya zauna a Najeriya? Yanzu jakadan Nijar da ofishin jakadanci na aikinsa ba tare da wata matsala ba inda babu alaka hakan zai yiwu? To ba gaskiya bane ace babu alaka.”
Sakamakon Bincike:
Binciken kafar bindiddigi na Alkalanci saboda kasancewar ma’aikatun harkokin kasashen waje na kasashen biyu sun tabbatar da alaka a hukumance kuma har ya zuwa lokacin da akai ikirarin kasashen biyu nada jakadu a tsakani kuma jami’an gwamnatin kasashen biyu na ziyartar tare da tattaunawa da juna, kuma babu wani abu akasin hakan. Kafar Alkalanci ta yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.
Akwai Shirin Kafa Sansanin Sojan Faransa a Najeriya?
A bidiyon dai akwai ikirarin cewa kasar Faransa da Najeriya na shirin kafa sansanin soji a iyakar Nijar da Najeriya.
Kan wannan ikirari na samar da sansanin sojin Najeriya da Faransa a iyakar Nijar, mai magana da yawun ministan harkokin wajen Najeriya Alkasim Abdulqadir yace wannan ikirari ne da bashi da tushe balle makama. “Babu wani shiri na samar da sansanin sojin wata kasa a Najeriya kasar Faransa ce ko Amurka babu wannan maganar ballantana ace wai a iyakar Nijar da tun kafin turawan mulkin mallaka arewacin Najeriya suke da alaka ta auratayya, addini, yare, al’ada tsakanin mutanen, ta yaya ma hankali zai dauka.”
kafar bindiddigi ta Alkalanci ta tuntubi Ofishin jakadancin Faransa a Najeriya inda mai bada shawara a kan harkokin siyasa, Bertrand de Seissan, ya musanta ikirarin cewa Faransa na shirin samar da sansanin soji a Najeriya. “Babu wani shiri na samar da sansanin soji a Najeriya kwata.”
Da ma dai hukumomin kasar Nijar sunsha yin wannan zargi tun bayan ficewar sojin Faransa daga Nijar wanda hukumomin Najeriya da Faransa suka karyata.
Sakamakon bincike:
Kasancewar babu wata cikakkiyar hujja a rubuce ko a faifan sauti ko bidiyo dake nuna cewa an kammala wannan shiri kamar yadda mai ikirarin yayi, kafar bindiddigi ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa wannan ikirari ba gaskiya bane.
Najeriya Na Dakile Cigaban Nijar?
A cikin bidiyon dai akwai ikirari dake cewa Najeriya na dakile cigaban kasar Nijar.
Alkalanci yabi diddigin wannan ikirari inda ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ta bakin mai magana da yawun ministan harkokin kasashen waje Alkasim Abdulqadir yace; “Mutanen da ba su da aikin yi ne ke yin wannan maganganu marasa ma’ana a kafafen sada zumunta irin su TikTok don cimma wata manufa ko karkatar da hankulan al umma, kuma sunayin hakanne domin bata sunan Nijeriya da shugabannin ta, musamman ta irin wannan hanyar yin iƙirari marasa tushe, bai kamata jama’a su kula irin wadannan mutane ba domin bata lokaci ne.”
Ma’aikatar ta kara da cewa; “Najeriya a halin yanzu na kokari ne wajen an sami tare da tabbatar da ci gaban dukkan kasashen yammacin Afirka, ciki har da Nijar, wanene ba ya son makwabcinsa ya wadata? Annabi yace ka sowa dan uwanka abinda kake so wa kanka. Sannan kada ka manta a manufofin kasashen wajen na Najeriya wato foreign Policy na farko shine cigaban kasashen Afrika.”
Shi kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Nijar Amadou Ango Souley yace suma a hukumance suna wannan zargi domin; “Matsalar abinda muke gani na kokarin dakile Nijar ya fara ne daga lokacin da akai juyin mulki, musamman yadda Najeriya ke neman hada kai da Faransa. Ko kwanakin baya ai ministan mu da suka gana da ministan harkokin wajen Najeriya ya fada masa haka, kuma ya fada masa cewa Muna da hujjoji, kuma yace masa a daina irin wanga abu, mu Nijar bama son tashin hankali. Abinda zan iya cewa kenan domin bayanin ministan namu yana nan kan internate. Wannan matsala tsakanin gwamnati ne ba tsakanin ‘yan Najeriya da Nijar ba babu wanda zai iya rabamu.”
Sannan binciken Alkalanci ya gano cewa ikirarin dakile cigaban kasar Nijar ya samo asali lokacin da ECOWAS ta sanyawa Nijar takunkumi wanda Najeriya ta kashe wutar lantarkin da take baiwa Nijar tare da rufe iyakokinta da Nijar.
Haka zalika binciken Alkalanci ya gano cewa akwai ikirarin cewa tun daga lokacin juyin mulki da korar dakarun Faransa daga Nijar ne dai kasar Faransa ta fara gyara tare da karfafa alakarta da Najeriya wanda yasa kasar Nijar ke kallon hakan a matsayin makarkashiya.
Sakamakon Bincike:
Binciken Alkalanci baya ga tabbatar da cewa Najeriya shekaru da shekaru na kokarin kawo zaman lafiya da cigaban kasashe musamman a yammacin Afrika babu wani sahihin bayani‘ dake nuna Najeriya na dakile cigaban kasar Nijar tuntuni da akai ikirari, duk da cewa yanzu akwai alaka dake kara karfi tsakanin gwamnatin Najeriya da Nijar. Haka zalika Najeriya na kokari wajen ganin Nijar ta dawo kan turbar Damakradiyya wanda gwamnatin sojin Nijar ke ganin hakan a matsayin makarkashiya. Wannan yasa Alkalanci ya yanke hukuncin cewa wannan ikirari ne na kawar da hankali wato misleading a turance.