BindiddigiYaushe Khadijah AbdulHameed Taki Musabaha Da Shugaban Bankin UBA?

Yaushe Khadijah AbdulHameed Taki Musabaha Da Shugaban Bankin UBA?

-

Gidauniyar bankin UBA dai na daukar nauyin gasar rubutun insha’i wato essay competition, shekaru sama da goma, wanda yara ‘yan makaranta kan shiga.

Batu:

A tsakanin asabar 23 zuwa lahadi 24 ga watan Nuwamban shekarar 2024 ana ta yada hoton wata yarinyar mai suna Khadijah AbdulHameed wacce ake ikirarin taki yin masabaha da shugaban bankin UBA bayan tazo na biyu a gasar saboda addininta na musulunci bai bata dama ba.
Wani shafin Facebook mai suna Jaridar Arewa ya wallafa wannan labari a ranar lahadi 24/11/2024 a matsayin labarin daya faru a ranar. “ DA ƊUMI-ƊUMI: “Addini na ya hana hakan” Khadijah taƙi amincewa da musafaha da shugaban bankin UBA Sunanta Khadijah Abdulhamid, Husna daga makarantar Sakandaren Sweet Haven ta Jihar Kano, ta ki amincewa da musafaha da Oliver Alawuba, Shugaban Kamfanin UBA, a wajen gabatar da lambar yabo ta UBA Foundation Nigeria, inda ta ce Addininta ya hana hakan. Daga Usman Umar Katsina
Wannan hoto dai na cigaba da yaduwa inda ake nuna cewa abun ya faru ne a wannan shekarar ta 2024.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.

Bincike:

Kafar bindiddigi Alkalanci ta bincika hoton inda ta samo cewa wannan hoto an fara yada shine a watan Nuwamban bara wato 2023 lokacin da Khadijah AbdulHameed tazo ta biyu a gasar gidauniyar UBA karo na goma sha uku. A gasar dai Khadija ta sami kyautar Naira miliyan Uku.
A wancan lokaci mutane da dama sun yada wannan hoto dauke da bayanin yadda taki yin musabahar.
Alkalanci ta bincika hoton inda ta samo cewa wannan hoto an fara yada shine a watan Nuwamban bara wato 2023
Alkalanci ta bincika hoton inda ta samo cewa wannan hoto an fara yada shine a watan Nuwamban bara wato 2023

Sakamakon Bincike:

Binciken kafar Alkalanci ta tabbatar da cewa tabbas hoton gaskiya kuma ya faru, kuma Khadijah ta wakilci makarantar ta Sweet Haven dake Kano, to amma ba a wannan shekarar ta 2024 ne ya faru ba. Don haka ikirarin ko labarin dake nuna a wannan shekara ta 2024 abun ya faru ba gaskiya bane.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar