Shekara da shekaru akwai takaddama da takun saka tsakanin kasar Amurka da Rasha inda kowannen su ke son baza capacity da nuna karfin iko a duniya.
Batu:
Akwai labari a manyan jaridun duniya dama na Najeriya dake yaduwa na cewa shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump ya sami tattaunawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan batun yaki da ake ta gwabzawa tsakanin Rashan da kasar Ukraine.
An dai gano jaridu irin su BBC Hausa, Aminiya, Daily Nigeria Hausa sun wallafa wannan labarin.
Ga link din labarin BBC Hausa a nan.

Ga na jaridar Aminiya a nan.

Ga kuma na Daily Nigeria Hausa a nan.

Bincike:
Alkalanci ya fara bincike a kafafen yada labaran kasar Rasha domin samun nasu labarin kan wannan ikirari kan tattaunawar tsakanin shugabannin biyu da ake.
Kafar jarida ta TASS wacce mallakin kasar Rasha ce ta bayyana a shafinta cewa rabon da shugaban Rasha Vladimir Putin yayi magana da wani shugaban Amurka tun ranar 12 ga watan Fabrairun 2022 da yayi da shugaba Joe Biden kan batun Ukraine da alaka tsakanin kasashen biyu.
Haka zalika mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya musanta wannan zantawa inda ya bayyanata da cewa “karya ce tsagwaronta, Ko kuma kagaggen labari.”

Sannan Alkalanci mun duba me kasar Ukraine ke cewa Kan wannan ikirari inda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Ukraine tace bata da masaniya kan cewa anyi
wata tattaunawa tsakanin shugaba Trump da shugaba Putin.
wata tattaunawa tsakanin shugaba Trump da shugaba Putin.

Alkalanci mun bincika don samo abinda shi Trump Ko makusantan sa suke cewa kan wannan labari, to sai dai duk gidajen jaridun Amurka sun rawaito cewa daraktan yada labaran Trump wato Steven Cheung yaki cewa komai dangane da wannan ikirari.
Shi dai wannan labari alkalanci ya ga no cewa kusan dukkan jaridun sun samo shine daga jaridar Washington Post wanda itama jaridar tayi amfani da cewa ta samo labarin daga majiya mai karfi wato sources a turance inda a irin wannan ba’a fadin waye majiyar.
Sakamakon Bincike:
Bisa lura da binciken da alkalanci yayi na rashin samun tabbacin wannan tattaunawa tsakanin shugaban Trump da shugaba Putin musamman yadda kasar Rasha ta musanta wannan tattaunawa, haka zalika kasar Ukraine ma tace bata da masaniya musamman yadda a rahoton akace an sanar da ita kafin tattaunawar, sai kuma yin shiru daga shugaba Trump da na kusa dashi.
Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci bazata iya tabbatar da gaskiya ko akasin hakan ba dangane da wannan ikirari.
Tambahi: Munyi gyara kan hukuncin wannan bincike domin kasa samun dukkan bangarorin da abun ya shafa.