BindiddigiIna Gaskiyar Cewa Farfesa Maqari Ya Zama Wanda Yafi...

Ina Gaskiyar Cewa Farfesa Maqari Ya Zama Wanda Yafi Kowa Ilimin Hadisi A Afrika?

-

Suma malaman addini basu tsira ba wajen yada labaran karya akan su.

Batu:

Wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani labari cewa Farfesa Ibrahim Maqari na Najeriya ya zama dan Najeriya na farko da yafi kowa ilimin hadisi a Afrika.
Ɗan Najeriya ya zama mutum na farko da yafi kowa ilimin Hadisi a Afrika.
An zaɓi Farfesa Sheikh Prof. Ibrahim Maqari  daga Najeriya a matsayin wanda yafi kowa ilimin sanin Hadisan MANZON ALLAH SAW a kaf nahiyar Afrika. Barbara Jami’ar Musulunci ta farko wato  Al’azahar dake ƙasar Masar ta ayyana babban limamin Najeriya Professor Ibrahim Maqari a matsayin wanda yafi kowa ilimin sanin Hadisan MANZON ALLAH SAW da Fiqhu.”
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.

Bincike:

Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta binciki wannan ikirari inda ta gano cewa an fara yada labarin a ranar 3 ga watan Disembar 2023, yayin da shi kuma hoton an fara amfani dashi a watan Fabrairun shekarar 2022.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.
Sannan kafar Alkalanci ta tuntubi kanin Farfesa Ibrahim Maqari mai sun Fuad Maqari kan wannan labari dake yaduwa a kafafen sada zumunta inda ya fara tuntubar Farfesa Maqari wanda ya bashi damar yin magana a madadin sa kan wannan batu.
Fuad ya bayyanawa Alkalanci cewa; “Malam bai zo kusa da wannan batu ba, domin idan ana magana ta hadisi a Najeriya ma akwai Shaikh Shariff Saleh, kuma malamin Farfesa Maqari ne.
A yanzu Malam Sahihul Bukhari, da Muwadda Malik kawai yake karantarwa ma a fannin hadisi domin yafi mayar da hankali ga ilimin Fiqhu.”
Ya kara da cewa; “Wannan dai labarin karya ne, kuma ba labari ne da duk wani mai ilimi zai kula dashi ba, daliban malam ma dariya kawai suke. Maganar jami’ar Azhar kuwa ai ita Azhar nada malamai irin su malam sosoi, kuma Morocco da Aljeriya duk suna da irin malam dama wadanda suka fishi ilimin hadisi.”
“Tabbas kwanaki Malam yaje Morocco karbar kyauta, wannan kyauta ba tashi bace, ya karba a madadin shaikh Shariff Saleh ne. Wani abu da mutane basu sani ba ko wannan taron ma bashi da alaka da ilimin hadisi.

Sakamakon Bincike:

Kasancewar labarin dama sabun tashi akayi shekara guda bayan an fara yada shi kuma shi kansa Farfesa Maqari ta bakin kaninsa sun bayyana cewa babu wani abu makamancin haka daya faru tare da ayyana ikirarin a matsayin karya. Haka zalika babu wata kafar yada labarai sahihiya ta kowanne yare data yada irin wannan labari wanda yasa kafar bindiddigi ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa wannan labarin karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar