BindiddigiShin Gaskiyane Mali Ta Fita Daga Kangin Bashin Kasashen...

Shin Gaskiyane Mali Ta Fita Daga Kangin Bashin Kasashen Waje?

-

Hausawa sukace bashi hanji ne… wato yana cikin kowa- Kasashen Afirka na cikin kasashen duniya dake karbar basussuka daga bankunan kasa da kasa dama kasashe kansu.

Batu:

Wani shafi mai suna Daily News Hausa 24 ya wallafa cewa; “ A daidai lokacin da Nigeria ke kara ciyo dinbin bashi daga kasashen waje, sai gashi  Yanzu haka ƙasar Mali babu kasar da ke binta bashi duk duniya.
Yaushe kuke ganin Nigeria za ta gama biyan bashin da ake bin ta ?”
Wasu shafuka sun wallafa irin wannan rubutu kuma ya sami shares da dama.

Bincike:

Alkalanci yayi bincike kan wannan ikirari inda muka fara da duba kome asusun bada lamuni na IMF ke cewa Kan bashin da ake bin kasar Malin.
Mun gano cewa ya zuwa shekarar 2022 bashin kasashen waje dake kan kasar Mali ya haura dala biliyan shida ($6,342,843,423)) a bara dai asusun bada lamunin na IMF ya nuna damuwa kan yadda Mali ke samun karuwar basussuka.
Sannan mun duba shafin bankin duniya inda muka samo jerin bankuna dama kasashen dake bin kasar Mali bashin wanda ya hada da bankin duniya, bankin bunkasa Afrika, bankin bunkasa yammacin Afrika, gwamnatin Faransa, Chana, Indiya, Abu Dhabi. Kuma kashi 30 na bashin daga kasashen wajen a kudin Euro ne a cewar rahoton bankin duniya.
Bamu tsaya anan ba mun bincika me ita gwamnatin Mali ke cewa Kan basussuka, sai muka samo bayanin ministan tattalin arzikin kasar Alousseni Sanou inda yace kasar na kokarin biyan bashin cikin gida daya kai dala miliyan dari uku da talatin da uku ($332 million).
Sannan bankin bunkasa nahiyar Afrika ya fitar da jerin kasashen da bashinsu bashi da yawa wanda kasar ta Mali bata ciki.

 

Sakamakon Bincike:

Bisa wadannan alkaluma da bincike da Alkalanci yayi inda ya kasa samo sahihan labari Ko ikirari dake nuna cewa kasar ta Mali ta zama kasar da ba’a binta  bashi ya nuna cewa wannan labari karya ne domin kuwa babu wata kafar yada labarai sananniya a Afrika Ko a wajen Afrika data rawaito wannan labari duk da girman irin wannan labari.
 
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar