Hukunci: Ƙarya ne
Binciken Alkalanci ya tabbatar da cewa mashahuran shugabannin duniya sun kwanta a asibitin London Clinic kuma asibiti ne mai zaman kansa da yake kan gaba waje kwarewa a kaf kasar Burtaniya. Asibitin na da kwararrun likitoci surgeons da kwararrun masana lafiya sama da dari bakwai da kuma masu kula da lafiya da ma’aikata 1,300. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa asibitin karami ne karya ne.
Asibitin London clinic da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu dai asibiti ne dake kasar Burtaniya.
Wasu mutane a Najeriya saboda da sunji ance “Clinic” na maganar cewa Buhari ya mutu a wani karamin asibiti a Landan.
Akwai wani malamin addinin musulunci a Jos da ya yayi ikirarin cewa asibiti karami ne matuka.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci tayi bincike kan shin karamin asibiti ne kamar yadda ake fada ko yaya?
Yaushe aka bude asibitin?
Asibitin London Clinic dai an bude shi a shekarar 1932 wato ya zuwa yanzu ya kusa shekaru dari da kafuwa.
Inda asibitin yake
Da farko dai asibitin mai suna London Clinic na babban gininsa a gini mai lamba 20 Devonshire Place London W1G 6BW.

Sannan akwai wani reshe da suke kira The Duchess of Devonshire wing dake gini mai lamba 22 Devonshire Place London W1G 6JA. Sauraniyar Ingila Queen Elizabeth ta biyu ita ce ta bude wannan reshe a shekarar 2010.

Dakunan ganin likita ko duba marasa lafiya na asibiti London Clinic su kuma suna gini mai lamba 5 Devonshire Place London W1G 6HL.

Akwai wasu dakunan ganin likita dake gini mai lamba
116 Harley Street London W1G 7JL.
Sanannun mutane da suka taba kwanciya a asibitin
Akwai manyan shugabannin duniya da suka taba kwanciya a wannan asibiti na London Clinic.
Misali a shekarar 2024 Sarkin Ingila Charles ya kwanta a wannan asibiti na London Clinic, don masa aiki kan kansar mafitsara.
‘Yarsa Law Ket itama a wannan shekarar ta kwanta a wannan asibiti na London clinic.
Tsohon shugab kasar Amurka John Kennedy shima ya taba kwanciya a wannan asibiti na London clinic.
Yawan ma’aikatan da kudin gudanar da asibitin
A rahoton asibitin na shekarar 2023, asibitin na da kwararrun likitoci da ake kira surgeons da kwararrun masana lafiya 750. Haka zalika akwai sauran ma’aikatan lafiya da ma’aikatan asibitin da suka kai 1,300.

Asibitin London Clinic dai anyi ittifakin cewa yana cikin na daya zuwa na uku na asibitoci masu zaman kansu da suka fi iya aiki da kwarewa a kaf Burtaniya.
Asibitin London Clinin na kashe kudin daya kai Pound miliyan casa’in da daya (£91m) wato sama da Naira biliyan dari da tamanin da shida (N186,498,403,000)
wajen biyan ma’aikatan sa a shekara. Yana kuma kashe Pound miliyan dari da saba’in da uku (£173m) wato sama da Naira biliyan dari uku (N354,586,163,000).
wajen gudanar da asibitin.
wajen biyan ma’aikatan sa a shekara. Yana kuma kashe Pound miliyan dari da saba’in da uku (£173m) wato sama da Naira biliyan dari uku (N354,586,163,000).
wajen gudanar da asibitin.
Asibiti har ila yau yana kashe kudin daya kai pound miliyan goma sha daya (£11m) wajen bada tallafi wato Charity.

Sakamakon bincike: