Fayyace abubuwaYadda Wasu Ke Shammatar Gidajen Jaridu Wajen Yada Labaran...

Yadda Wasu Ke Shammatar Gidajen Jaridu Wajen Yada Labaran Karya

-

Labaran karya Ko labaran kau da hankula koma labaran yaudara yana neman zama ruwan dare a harkar tsaro dama yaki da yan bindiga a Najeriya.
Shafukan sada zumunta sun zama matattarar yada labaran karya da wanda akeyi don kauda kan mutane Ko yaudarar jami’an tsaro.
Suma yan bindiga ko bata gari sun fahimci  tasiri da shafukan sada zumunta keyi wajen yada ko kauda hankula wato misleading mutane.
An sha samun faya-fayen bidiyo da ake yadawa kan kodai ‘yan bindiga Ko kuma jami’an tsaro wanda bincike ke nuna cewa kodai tsohon bidiyo ne, tsohon hoto ne koma dai ba a Najeriya akai abinda ake ikirarin ba.
An sha wallafa bidiyon ikirarin ankai hari wasu garuruwa amma daga baya ko dai jama’an tsaro su musanta hakan ko kuma mutanen garin su musunta.
Dama dai shi yada labaran karya ko na kauda hankalin mutane anayin sane domin cimma wata manufa.

Gidajen Jaridu Basu Tsira Ba!

Baya ga shafukan sada zumunta dake yada irin wadannan labarai abun na kara girmama domin kuwa gidajen jaridu suma basu tsira ba domin kuwa ana samun mutane masu wata manufa suna shammatar gidajen jaridun da mutane suka aminta dasu wajen yada ikirari ko labaran karya.
A shekarar nan ta 2024 an sami labarai ko muce ikirari na karya da dama kan harkokin tsaro a arewa maso yammacin Najeriya.
Masu yada labaran ko ikirari na karya sun shammaci manyan gidajen jaridu Hausa fadawa tarkon su.

Labarin Kashe Dogo Gide

A ranar 27 ga watan Mayu gidan radiyon VOA Hausa ya wallafa labarin cewa kasurgumin dan fashin dajin nan Dogo Gide ya mutu.
A rohoton dai anyi amfani da majiya. Wannan labari ya yadu matuka tare da sanya mutane da sama farin ciki a wannan lokaci, harma wasu suka dinga sanya hoton gawar da suke ikirarin tashi Dogo Gide ce, to amma daga baya labarin ya zamo ba gaskiya ba. 
Labarin Kashe Dogo Gide
Labarin Kashe Dogo Gide

Labarin Kama Baleri A Nijar

Haka zalika a ranar 29 ga watan Mayun 2024 BBC Hausa itama ta fada tarkon labarun kauda hankali wato misleading inda aka wallafa rahoton cewa sojojin kasar Nijar sun kama Dan bindigan da sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo wato Baleri Fakai, shima wannan labari ya yadu matuka to amma daga baya ya zama ba gaskiya ba, bayan da jaridar PRNigeria tabi diddigi wato fact-check kuma ta gano cewa wanda aka kama yasha banban da wanda BBC da sauran jaridu suka yada. 

Labarin Kama Baleri A Nijar
Labarin Kama Baleri A Nijar

Mamaye Sansanin Soji a Jihar Neja

A watan Oktoba ma an sami wani ikirari da wani dan majalisa yayi a jihar Neja cewa yan bindiga sun mamaye wani sansanin horaswa na sojojin Najeriya a jihar. Shima wannan labari ya yadu sosai a gidajen jaridu wanda daga bisani rundunar sojin kasar ta karyata waccan labari tare da bayar da cikakken bayani kan halin da gurin Ke ciki, wato shima ikirarin dan majalisar akwai tasgaro.

Artabu Da Mutanen Bello Turji A Sokoto

Kwatsam a 15 ga watan Nuwamba 2024 sai aka kara samin wani labari na barin wuta tsakanin dakarun soji, yan banga da yan bindiga a wasu garuruwan Sokoto, wanda yayi ikirarin yace kwanaki uku kenan a lokacin ana fafatawa, harda karar wani abu da yayi ikirarin harbin bindigane.
To sai dai wannan ikirari ya bar baya da kura domin kuwa mazauna kauyikan daya fada sun karyata labarin sunce babu wani abu makamancin haka a wannan lokaci. Wani dan daya daga cikin garuruwan da mai ikirarin ya ambata mai Shan Usamah Abubakar Tarah yace  a ranakun da mai ikirarin ke cewa ana gumurzu sun kai kudin fansa don karbar wasu yan uwansu. Inda yake tambayar tayaya hakan zai faru Idan ana wancan fada? Sabanin yadda ta saba shalkwatar tsaron Najeriya taki cewa komai dangane da wannan ikirari ba.
Tambayoyin da mutane da Dama zasuyi Kan wannan ikirari sune; shi wanda yayi ikirarin me yake son cimma? Su mutanen kauyikan da suka musanta wannan ikirari me suke son cimma? Su kuma jami’an tsaro me yasa suka ki tabbatar Ko karyata wannan ikirari?

Kalubale Ga Gidajen Jaridu

Matsalar ikirarin daba gaskiya ba musamman a inda gidajen jaridu suka dogara kacokan da majiya wato sources na fara zama babban kalubale domin dama shi labarin karya ana samar dashi kuma a yada shi ne domin cimma wata manufa.
Ba kamar shekarun baya ba da akwai karancin cimma wani muradi wato motive, yanzu akwai bangarori da dama da kullum suke son samun wata dama don cimma wata manufa ta hanyar yada labarun karya wanda gidajen jaridu Idan basuyi taka tsan-tsan ba suma sai su fada tsundum ba tare da sun ankara ba.

Illar Labarun Karya Ga Mutane

Wani abu da mutane da dama watakila basu sani ba shine labaran karya ka iya rikitar da tunani, sanyaya gwiwa da kuma sanya shakku a zuciyoyin mutane a cewar masana halayyar dan Adam.
Wanda mutane da garin gudu ko neman mafita bayan sunji labaran karya kodai sun raunata, ko kuma sunyi asarar dukiya a yayin da wasu tuni sun yanke kauna wato hope daga samun mafita kan matsalolin tsaro a yankunan su.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar