Ana iya ganin macizai a gonaki, cikin ciyawa harma a kan bishiyoyi, domin kuwa manoma sunsha ganinsu kodai lokacin damuna ko a lambu lokacin rani.
Batu:
Akwai ikirari da hotuna dake yaduwa kamar wutar daji a kafar sada zumunta na Facebook ana cewa maciji na shan tumatir ko barin hakorinsa a jikin tumatir wanda Idan mutum yasha na iya mutuwa.
Wani mai suna Engr. Ibrahim Said Uba ya wallafa irin wannan ikirari inda ya sami shares sama da dari hudu inda yace; “ Jama a Idan Kaje Lambunka kaga irin wannan Tumatir din Akiyaye shansa , da yawansu Majijai ne suka shasu, kuma sukan zuba Guba lokacin da suke Shan su.”

Shima Wani mai suna Hassan Suleiman ya wallafa ikirari tare da hotuna inda ya sami shares sama da dubu daya da dari hudu, a ikirarin yace; “ Jama’a don Allah idan anga irin wannan tumatur akiyayeshi, domin macijine yasaka hakorinshi, kuma wanda jininshi baida karfi idan yaci wannan tumatur wallahi bazai kwanaba sabida irin gubarda yake dauke dashi.”

Bincike:
Alkalanci mun fara da tuntubar likitan dabbobi Dakta Sani Hamidu Kwairanga inda yace ai su macizai bama sa cin tsirrai ko ganye balle kayan marmari. “ Su macizai ana saka su a dabbobi dake cin nama ne kadai wato carnivorous a turance dan haka babu wata ingantacciyar masaniya na cewa suna cin ganye ko tsirrai balle susha tumatur, sai dai wata kila kokarin cin wasu kwari tunda tsutsotsi na cin tumatir sai su gatseshi kaga kuwa bazai zama irin yadda yake a hoton nan ba.” Ya kara da cewa “saboda cututtuka da dabbobi ke dauke dasu Idan dabba tayi wani mu’amala Ko wasa kusa da wani abinci to sai anyi taka tsan-tsan bawai maciji kadai ba.”
Alkalanci mun tuntubi shugaban manoma tumatir na jihar Kano kuma Sakataren kungiyar manoma tumatir ta Najeriya Sani Danladi Yadakwari inda ya karyata wannan labari; “Bamu taba samin labarin wai wani inda maciji yaje yaci tumatir har wani ya tsinka ya mutu ba. Asali ma maciji ba Shan tumatir yake ba. Kuma Idan ma maciji zai gatsi tumatir ba haka zai kasance ba kamar yadda ake nunawa a wannan hoton ba. Wannan hoto da kake gani sai dai Idan tsutsa ce ta shiga ta fita kamar tsutar da muke kira sharon Ko wata daban wannan labari babu gaskiya.“
Har ila yau Alkalanci mun kuma tuntubi masanin harkar noma Sulaiman Yantumaki inda yace maciji baya bula tumatur yayi huji mai zurfi, bayan yaga hoton da ake yadawa yace; “Wannan tsutsace, wacce take cin ganyen tumatur sune suke cin tumatur din musamman idan ya fara nuna. Baya ga wannan kana iya ganin huji guda daya, guda uku harma biyar a jikin tumatur daya.” Ya kara da cewa, “Tumatur ba abincin maciji bane kuma koda ace ma macijin ya sanya hakorinsa to tumatur din zai lalace dandanan koda kuwa bai nuna ba balle ace ya nuna.”
Ita kuwa wata masaniyar harkokin noma Ameera Mato turo mana hoton yanayin da tumatir kan kasance Idan maciji yayi wasa dashi wanda yasha banban da wancan da ake yadawa.

A binciken mu mun gano cewa an yada irin wannan labari a kasar Masar inda ya tilasta kungiyar manoman kasar fitar da sanarwar karyata irin wannan labari.
Sakamakon Bincike:
Bisa binciken da Alkalanci yayi ya tabbatar tare da yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne domin kuwa yaci karo da ilimin masana lafiyar dabbobi, noma dama su kansu manoman.