Gwamnatin kasar Nijar dai na cigaba da zargin gwamnatin Najeriya wajen cewa tana hada kai da kasar Faransa domin tada hargitsi a kasar ta Nijar. Wadannan zarge-zarge dai na zuwa da ikirarin karya.
Batu:
Akwai wani bidiyo dake yaduwa a kafofin sada zumunta da dama dake nuna shugaban mulkin soji na kasar Nijar yana hira da wani dan jarida inda a ciki yayi ikirarin cewa;
Shugaban Najeriya ya amshi kudi daga Faransa domin basu guri a Borno inda suka kafa wani sansanin soji gurin da suke kira “Canada”.
Bincike:
Binciken da kafar bindiddigi ta Alkalanci tayi tun kwanakin baya ya tabbatar da cewa babu sojin Faransa a jihar Borno balle ma kafa sansani.
Sabon bincike bayan wannan bidiyo wanda ya hada da tuntubar dakarun sojin Najeriya dake aiki a jihar Borno ya tabbatarwa da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci cewa babu wani sojin Faransa dake yankunan Kurnawa, Kangarwa da Dogon Chikun da shugaban na Nijar yayi ikirari a bidiyon. Domin kuwa yanki ne da ‘yan kungiyar ISWAP ke kai farmaki sosai.
A kwanakin baya ma dai shalkwatar tsaron Najeriya ta musunta shirin kafa sansanin sojin wata kasa a Najeriya wanda aka dinga yada tsohon bidiyo sojin Birtaniya a matsayin sojin Faransa.
Mai magana da yawun ministan harkokin wajen Najeriya Alkasim Abdulkadir shima ya musunta samar da sansanin sojin Faransa mai suna CANADA a jihar ta Borno. “Tabbas shugaba Tinubu yaje Faransa wanda kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi irin lafiya, sanya hannun jari, sufuri, noma da lantarki haka kuma akwai ‘yan kasuwar Najeriya da suma suka sanya hannu domin fara bude kasuwancin su a Faransa . Najeriya kasace mai tasowa kuma ta sanya irin wannan yarjejeniya da kasashe irin su China, America, Rasha da Japan.”
Ofishin jakadancin Faransa a Najeriya shima ya musunta shirin samar da sansanin soji a Najeriya.
Sakamakon bincike:
Bisa kasa samun wata hujja ta wanzuwar ko samuwar sansanin soji balle sojin wata kasa a yankin da shugaban na Nijar ya ambata yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin karya ne.