Fayyace abubuwaMenene cin zarafi ko wulakanta takardar Naira?

Menene cin zarafi ko wulakanta takardar Naira?

-

Labarin daure shahararriyar ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya da kotu tayi na wata shida da kuma wani ango a kwanakin baya mai suna Abdullahi Musa, wanda dukkan su  saboda sun wulakanta ko ace sunci zarafin takaradar Naira ta hanyar watsi da kuma liki, zai sanya mutane da dama canza yadda suke lika kudi lokacin bukukuwa.
A watan Janairu ne dai hukumar EFCC ta kama Murja Kunya bisa zargin cin zarafin takardar Naira ta hanyar watsi lokacin da take zaune a otel din Tahir dake Kano.
A ranar 28 ga watan Mayu 2025 wata kotu a Kano ta yanke hukunci tasa keyar Murja zuwa gidan gyara hali har na tsawon watanni shida.
 A watan Afrilun da ya gabata ne dai kotu a Kano ta yanke hukuncin daure Abdullahi Musa na watanni shida bisa tuhumarsa da hukumar EFCC tayi na cin zarafin takardar Naira, a ranar bikin sa.
Lika kudi ne kadai wulakanta Naira?
Akwai dokar dake kula da yadda ya kamata ayi da takardar Naira lokacin bukukuwa. Dokar babban bankin Najeriya ta shekarar 2007 ta bayyana, liki, rawa a kan takardar Naira na iya sanya a daure mutum na watanni shida ko tarar Naira dubu hamsin (N50,000) ko kuma ma duka biyun.
Dokar sashe na ashirin da daya, biyar cikin baka [ 21(5)(ii)] ya bayyana haramcin; “lika ko watsa takardar Naira ta hanyar ado, ko likawa a kowanne sashe na jikin mutum ko watsa kwandaloli koda kwabo ne a biki.”
  Baya ga batun liki akwai sauran abubuwan da suka zama laifi wanda na iya sanya mutum samun matsala da hukumar EFCC ko CBN.
Wadannan abubuwa da suka kasance cin zarafi ko wulakanta Naira sun hada da; rubutu a kan takardar Naira, yaga wa ko yage wani bangare na takardar Naira, kudundune takardar Naira, like takardar Naira a allo ko bango, yin ado da takardar Naira, misali sanya takardar a cake din bikin tunawa da ranar haihuwa, ko jera takardar Naira kamar fulawa wato fure, siyar da sabbin takardun Naira a guraren biki, taka takardar Naira lokaci rawa.
Duk wadannan sun kasance laifukan da ka iya sanya mutum ya sami hukuncin daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ko ma duka biyun.
Don haka Idan kuma tunanin yin liki da takardar Naira ko daya daga cikin laifukan da muka bayyana ku tuna cewa zaku iya zaman gidan gyara hali na watanni shida?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Karanta wannan

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar