BindiddigiKarya: Jirgin Mahajjatan Mauritania baiyi hatsari ba

Karya: Jirgin Mahajjatan Mauritania baiyi hatsari ba

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa karyata faruwar hatsarin da kamfanin jirgin na Mauritania yayi da kuma rashin samun labarin a wata sahihiyar kafar yada labarai. Sannan hotunan da ake amfani mafi akasari hadin AI ne sa kuma wanda aka wa kwaskwarima yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa karya ne.
Labarin hatsarin jirgin sama dauke da mahajjatan kasar Mauritania ya yadu matuka a shafukan sada zumunta. Tuni dai kamfanin jirgin saman na Mauritania ya musanta labarin ta shafin sa na Facebook da harshen larabci.
Wani shafin Facebook mai suna Mansur Ahmad ya wallafa ikirarin cewa;
“Wani jirgin Mahajjata na ƙasar Mauritania ya samu haɗari inda duka mahajjatan Mutum 210 suka riga mu gidan gaskiya.”
Labari da hoton karya da ke cigaba da Yaduwa
Wani shafin ma mai suna Voice of  Islamic shima ya wallafa wannan labari inda sama da mutane dari biyu sukai sharing.
Labari da hoton karya da ke cigaba da yaduwa
Wani shafin da ban shima ya wallafa wannan labari.
Labari da hoton karya da ke cigaba da yaduwa
Bincike:
Kafar tantance labarai ta duba shafin kamfanin jirgin sama na kasar ta Mauritania inda kamfanin ya karyata labarin wannan labari.
Bayanin karya labarin hatsarin jirgi a shafin kamfanin jirgin saman Mauritania
Sannan Alkalanci ya tantance hotunan hatsarin da ake yadawa ta amfani da manhajojin tantance hotuna inda ya gano cewa akwai wadanda akai hadin AI da kuma wanda akai yiwa tsoffin hotunan hatsarin jirga kwaskwarima domin a nuna cewa an sami hatsarin.
Sakamakon bincike:
Bisa karyata faruwar hatsarin da kamfanin jirgin na Mauritania yayi da kuma rashin samun labarin a wata sahihiyar kafar yada labarai. Sannan hotunan da ake amfani mafi akasari hadin AI ne sa kuma wanda aka wa kwaskwarima yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar