BindiddigiMe yasa shugaban Nijar ke zargin Najeriya ba tare...

Me yasa shugaban Nijar ke zargin Najeriya ba tare da fito da hujjoji ba?

-

Tun bayan juyin mulki da sojoji sukayi a ƙasar Nijar Shugaban ƙasar Abdurahaman Tiani ke takun saka da kasar Najeriya inda ya sha zargin Najeriya da aiki tare da ƙasar Faransa don hargitsa ƙasar Nijar.
A watan Disambar bara ya yi wasu zarge-zarge da bincike a wancan lokaci ya nuna cewa akwai ƙarairayi a cikin zarge-zargen.
Najeriya ta hana fitar ko shigar da kaya Nijar? 
Shugaban ƙasar na Nijar Janar Tiani a wata hira da gidan jaridar kasar da ya fito kafafen sada zumunta a ranar 31/5/2025  an kara jin shi yana wasu iƙirari kan Najeriya da wasu kasashen Afrika.
Ya ce hukumomin Najeriya sun hana fitar da kaya zuwa Nijar ko shigo da abubuwa daga ƙasar Nijar.
To sai dai akasin abinda ya faɗa Najeriya bata hana fita ko shigowa da halastattun abubuwa ba.
Da ma dai Najeriya ta hana shigo da motoci ta iyakokin ƙasa tun shekaru da dama da suka gabata.
Binciken kafar tantance labarai ta Alkalanci ya nuna cewa hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya ta samawa Najeriya kuɗaɗen shiga daga iyakokin Najeriya da Nijar da dama.
Haka zalika Najeriya ya zuwa yanzu bata hana shige da fice tsakanin ƙasashen biyu ba.
Mai magana da yawun ministan harkokin wajen Najeriya Alkasim Abdulkadir ya bayyanawa Alkalanci cewa Najeriya bata taɓa umartar jama’anta da kada su bari a shiga da wani abu halastacce daga Nijar ko kuma wani abu daga Najeriya, tun bayan ɗage takunkumi da Najeriya ta cire wa Nijar.
Hasalima gwamnatin ƙasar ta Nijar ita ce ta hana shigar da wasu kayayyaki zuwa Najeriya.
Akwai kuma lokuta da dama da jami’an ƙasar ta Nijar suka hana ƴan Najeriya shiga duk da suna da cikakkun takardu.
Zargin taro tsakanin jami’an ƙasashen Afrika ta yamma, Faransa da ƴan ta’adda a Abuja.
Wannan dai shine karo na biyu da shugaban ƙasar yake zargin cewa Najeriya na haɗa kai da ƙasar Faransa wajen birkata Nijar.
To sai dai wannan iƙirarin na shi bai gabatar da wasu kwararan shaidu ba.
Wasu ƴan ƙasar ta Nijar dai na gani cewa zarge-zargen hanya ce ta barin jaki da daki taiki.
Binciken Alkalanci ya gano cewa an ƙara samun ƙarin hare-haren ƴan ta’adda a ƙasar Nijar musamman a iyakokin ƙasar da Burkina Faso.
Daga ɗaya zuwa talatin da ɗaya ga wa Mayun da ya wuce ƙungiyoyin ƴan ta’adda a Nijar sun kashe sama da soji 180 sai kuma fararen hula sama da dari.
A Najeriya dai shalkwatar ƙungiyar ECOWAS take kuma ƙungiyar na gabatar da taruka iri-iri harda taron majalisar dokokin ƙungiyar da a wasu lokuta Sanatoci da ƴan majalisar wakilai kan yi zama domin tattaunawa.
Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya sha jaddada cewa Najeriya tunda aka kafata bata taɓa yin wani abu da zai cutar da wata ƙasa ba.
A matsayin Najeriya na ƙasa mai cin gashin kanta bazai yiwu wata ƙasa ta dinga katsalandan ko kuma ita ce zata iya sawa ko hana Najeriya alaƙa da wasu ƙasashe.
Shima dai zargin na shugaban Nijar kan taron maƙarƙashiya daya faɗa bai bayar da wata shaida ba fyace magana ta fatar baki.
Faransa na aiki da ‘yan ta’adda?
A cikin hirar ta sa ya yi iƙirarin cewa ƙasar Faransa ce take kitsa garkuwa da turawa a ƙasashen Sahel, ya ƙara da kiran wani suna Boubacrar Dabounguel a matsayin wanda ke yiwa Faransa aiki. Wannan zargi dai ya yishi ne ta fatar baki ba tare da gabatar da hujja ko ɗaya ba.
Ya kuma zargi cewa Faransa na goyon bayan wani ɗan ta’adda mai suna Iyad Ghali.
Binciken Alkalanci ya gano cewa sojojin Faransa ne dai suka dakatar da wannan ɗan ta’adda a shekarar 2013, tare da ƙona gidan sa ta hanyar jefa bam.
Tun korar sojojin Faransa da Amurka da gwamnatin sojin Nijar tayi basu koma ƙasar ba.
Wani mai sharhi a ƙasar ta Nijar dai ya ce waɗannan zarge-zargen anyi su ne don kawar da hankulan ƴan ƙasar daga halin taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Karanta wannan

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar