Tun bayan juyin mulkin kasar Nijar labarun karya kala-kala ke yaduwa kan kasashe daban-daban wanda ya hada da Tarayyar Turai.
Ikirari:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram post ya wallafa wani ikirari a ranar 18/02/2025 inda yake cewa; “Sabon passport din AES ya kasa yin tasiri a tarayyar Turai yayin da ƙasashen Schengen suka ki karbar sa kuma suka hana visar Turai ga masu passport din.”
Bincike:
A farkon shekarar nan ne dai akai rawaito cewa kasar Burkina Faso ta kaddamar da fasfo din kasashen AES bayan ficewar su daga kungiyar ECOWAS.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntubi mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijar Amadou Ango Souley yace wannan ba gaskiya bane. “Wannan labarin karya ne kawai, babu magana irin wannan. Idan da akwai irin wanga magana da mun fitar da sako ga manema labarai. Suma da sun sanar damu.”
Sannan mun tuntubi Tarayyar Turai inda aka tabbatar mana da cewa wannan ikirari ba gaskiya bane. “Bada visa ayyukan ofishin jakadancin kasashen ne, kuma kowacce kasa tana da tsari da kuma abinda take dubawa kafin ta bada visa ko ta hana.”
Sakamakon bincike:
Bisa bayanan ma’aikatar harkokin wajen Nijar da kuma jami’a daga kungiyar Tarayyar Turai na cewa babu wannan magana ta kin karbar fasfo din dake dauke da tambarin AES yasa kafar tantance labarai ta Alkalanci yanke hukuncin cewa karya ne.
Labarai masu alaka: