BindiddigiKasashen Turai Basu Ki Karbar Fasfo Din Kasashen AES...

Kasashen Turai Basu Ki Karbar Fasfo Din Kasashen AES Ba

-

Tun bayan juyin mulkin kasar Nijar labarun karya kala-kala ke yaduwa kan kasashe daban-daban wanda ya hada da Tarayyar Turai.

Ikirari:

Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram post ya wallafa wani ikirari a ranar 18/02/2025 inda yake cewa; “Sabon passport din AES ya kasa yin tasiri a tarayyar Turai yayin da ƙasashen Schengen suka ki karbar sa kuma suka hana visar Turai ga masu passport din.”

Bincike:

A farkon shekarar nan ne dai akai rawaito cewa kasar Burkina Faso ta kaddamar da fasfo din kasashen AES bayan ficewar su daga kungiyar ECOWAS.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntubi mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijar Amadou Ango Souley yace wannan ba gaskiya bane. “Wannan labarin karya ne kawai, babu magana irin wannan. Idan da akwai irin wanga magana da mun fitar da sako ga manema labarai. Suma da sun sanar damu.”
Sannan mun tuntubi Tarayyar Turai inda aka tabbatar mana da cewa wannan ikirari ba gaskiya bane. “Bada visa ayyukan ofishin jakadancin kasashen ne, kuma kowacce kasa tana da tsari da kuma abinda take dubawa kafin ta bada visa ko ta hana.

Sakamakon bincike:

Bisa bayanan ma’aikatar harkokin wajen Nijar da kuma jami’a daga kungiyar Tarayyar Turai na cewa babu wannan magana ta kin karbar fasfo din dake dauke da tambarin AES yasa kafar tantance labarai ta Alkalanci yanke hukuncin cewa karya ne.
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar