Hukunci: Ƙarya ne
Babu sahihan bayanai da suka nuna anyi juyin mulki a Ivory Coast, kuma bidiyo da hotunan da akai amfani da su tsoffi ne, wanda yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin anyi juyin mulki a kasar karya ne.
Akwai dai rahotanni da yawa dake yaduwa a kafafen sada zumunta inda ake ikirarin cewa anyi juyin mulki a kasar Ivory Coast.
Ikirari:
Ikirarin cewa anyi juyin mulki a kasar ta Ivory Coast wanda ke cigaba da yaduwa matuka a shafin Tiktok da Facebook wanda wannan shafin (( https://vm.tiktok.com/ZMSYAkfuG/ )) da wannan ((https://www.facebook.com/share/p/1An3PTTkmx/?))da wannan (https://www.facebook.com/share/v/16KRHtLczd/?) suka yada.

Shafukan da suka yada wannan labari da Alkalanci ta gani yawanci a kasashen Najeriya da Nijar suke.

Wani dan jaridan kasar ta Burkina Faso ya bayyanawa Alkalanci cewa shima ya ga labarin cewa anyi juyin mulki to amma ba gaskiya bane domin babu wani abu makamancin hakan.
Bincike:
Bisa kasa samun sahihin labarin cewa anyi juyin mulki a kasar ta Ivory Coast da kuma kura da cewa bidiyon da akayi amfani da su wajen nuna anyi juyin mulkin tsoffin ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin karya ne.
