Hukunci: Ƙarya ne
Bisa karyata faruwar hatsarin da kamfanin jirgin na Mauritania yayi da kuma rashin samun labarin a wata sahihiyar kafar yada labarai. Sannan hotunan da ake amfani mafi akasari hadin AI ne sa kuma wanda aka wa kwaskwarima yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa karya ne.
Labarin hatsarin jirgin sama dauke da mahajjatan kasar Mauritania ya yadu matuka a shafukan sada zumunta. Tuni dai kamfanin jirgin saman na Mauritania ya musanta labarin ta shafin sa na Facebook da harshen larabci.
Wani shafin Facebook mai suna Mansur Ahmad ya wallafa ikirarin cewa;
“Wani jirgin Mahajjata na ƙasar Mauritania ya samu haɗari inda duka mahajjatan Mutum 210 suka riga mu gidan gaskiya.”

Wani shafin ma mai suna Voice of Islamic shima ya wallafa wannan labari inda sama da mutane dari biyu sukai sharing.

Wani shafin da ban shima ya wallafa wannan labari.

Bincike:
Kafar tantance labarai ta duba shafin kamfanin jirgin sama na kasar ta Mauritania inda kamfanin ya karyata labarin wannan labari.

Sannan Alkalanci ya tantance hotunan hatsarin da ake yadawa ta amfani da manhajojin tantance hotuna inda ya gano cewa akwai wadanda akai hadin AI da kuma wanda akai yiwa tsoffin hotunan hatsarin jirga kwaskwarima domin a nuna cewa an sami hatsarin.
Sakamakon bincike: