BindiddigiIna Gaskiyar Cewa Shekaru 823 Ba’a Sami Watan Janairu...

Ina Gaskiyar Cewa Shekaru 823 Ba’a Sami Watan Janairu Mai Juma’a Biyar Ba

-

Ranar farko ta shekarar 2025 wasu sun fara da yada ikirarin karya kan watan Janairun shekarar.

Batu:

Wani shafin Facebook mai suna Hussaini Lawan Roni ya wallafa wani ikirari a ranar 1/1/2025 inda yake cewa “ Bayan shafe shekaru 823 a Tarihi ba a samu irin wannan ba sai a wannnan shekarar ta 2025 Musulmai za su yi Sallar Juma’a sau 5 cikin  Wata ɗaya. Wato cikin watan farako na Shekarar 2025. Allah buwayi gagara Misali.”
Hoton ikirarin karya dake cigaba da yaduwa.
Hoton ikirarin karya dake cigaba da yaduwa.
Shima wani shafin na Facebook mai suna Basiru A Shu’aibu ya wallafa wannan ikirari a ranar ta 1/1/2025 inda ya rubuta cewa “Bayan shafe shekaru 823 a Tarihi ba a samu irin wannan ba sai a wannnan shekarar ta 2025 Musulmai za su yi Sallar Juma’a sau 5 cikin  Wata ɗaya. Wato cikin watan farako na Shekarar 2025. Allah buwayi gagara Misali.”
((https://www.facebook.com/share/p/14aB7aq862/?)) wanna wallafa dai ta sami shares sama da goma cikin awanni biyu da wallafawa.
Hoton ikirarin karya dake cigaba da yaduwa.
Hoton ikirarin karya dake cigaba da yaduwa.

Bincike:

Da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta duba tsoffin kalandun kwanan wata ta gano cewa, anyi ranakun Juma’a biyar a watan Janairun 2021. Wanda ranakun Juma’a biyar din suka kama a 1/1/2021, 8/1/2021, 15/1/2021, 22/1/2021 da 29/1/2021.

Shekarar 2020

Sannan shekarar 2020 ma an sami ranakun Juma’a biyar a wantan Janairun wannan shekara inda ranakun suka zama; 3/1/2020, 3/1/2020, 17/1/2020, 24/1/2020, 31/1/2020.

Shekarar 2016

Itama shekarar 2016 an sami ranakun Juma’a biyar a watan Janairun ta wanda suka fada, 1/1/2016, 8/1/2016, 15/1/2016, 22/1/2016 da 29/1/2016.

Sakamakon bincike:

Bisa samun shekarun baya-bayan nan na 2021, 2020, 2016 wanda suke kasa da shekaru goma da suka gabata da aka sami ranakun Juma’a biyar a cikin su, wanda kuma musulmai kanyi sallar Juma’a yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannna ikirari na shekaru 823 ba’a sami watan Janairu da Muslimai sukai sallar Juma’a biyar a ciki ba karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar