Shekara da shekaru dai kasar Saudiyya na turowa Najeriya Dabino musamman gab da Azumin Ramadana a rabawa talakawa ko ‘yan gudun hijira.
Ikirari
Akwai wani bidiyo dake yawo a shafin sada zumunta na Tiktok mai suna @bello.galadanchi wanda aka wallafa a ranar 22/02/2025 inda wanda ke cikin bidiyon yayi ikirarin cewa dabino kadai Saudiyya ta turawa Najeriya bayan da ta sanya hannun jari na dala biliyan dari shida a kasar Amurka $600bn.
Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa watan Disembar 2024 an bayyana cewa kasar Saudiyya ta sanya kudi a harkokin kasuwanci a Najeriya daya kai dala miliyan dubu daya da miliyan dari biyu $1.2bn.
Sannan a watan Janairun wannan shekarar ta 2025 kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ya wallafa cewa kamfanonin kasar masu zaman kansu da jami’an gwamnatin Najeriya sun amince suyi aiki domin cigaba da zuba jari a Najeriya musamman a fannin ma’adanai, noma, kayan abinci, harkokin banki da fasaha.
A watan Nuwamban shekarar 2023 kasar ta Saudiyya da Najeriya suka amince da Saudiyya ta sanya hannun jari domin gyara matatun man Najeriya bayan da shugaba Tinubu ya ga na da Yariman Saudiyya Salman bn Yusuf.
Sannan kuma kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya kai Riyal miliyan dubu biyu da miliyan dari bakwai SAR 2.7bn.
Haka zalika kasar ta Saudiyya ta kashe kudi da ya ka dala miliyan arba’in da bakwai wajen bada agaji a garuruwa sama da 90 na Najeriya a cewar ofishin jakadancin kasar dake Najeriya.
Batun bada dabino dama dai kasar Saudiyya na ba wa kasashe dake da musulmai da yawa dabino duk lokacin azumi wanda ya hada da Najeriya. Idan za’a iya tunawa lokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari sai da aka sami wata badakala kan boye dabino da akayi aka rabawa makusanta gwamnati maimakon’yan gudun hijira.
Sakamakon bincike:
Bisa lura da wadannan alkaluma wanda ya nuna cewa kasar Saudiyya ta sanya makuden kudade a Najeriya kuma ba dabino ka dai take aikowa Najeriya ba yasa kafar tantance labarai ta Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin karya ne.
Labarai masu alaka: