BindiddigiBidiyon Shekarar 2013 Na Sojojin Najeriya Dana Faransa A...

Bidiyon Shekarar 2013 Na Sojojin Najeriya Dana Faransa A Mali Na Yaduwa A Matsayin Sabo

-

Tun bayan sabon zarge-zarge da gwamnatin kasar Nijar tawa gwamnatin Najeriya kan samar da sansanin sojin Faransa a wani yanki na arewacin Najeriya aka kara samun karuwar ikiraran karya a kafafafen sada zamunta.

Batu:

Wani shafin Facebook mai suna IG Wala ya wallafa tsohon wani  (archived here) bidiyo ranar 27/12/2024 dake nuna sojin Najeriya dana Faransa suna kwasar kaya daga jirgin sama inda ana iya ganin jirgin sojin Najeriya a bidiyon wanda ya rubuta cewa “Wadanne ‘yan gudun hijira ne wadannan masu kama da sojojin Faransa a Nigeria?😎 #Bamayi2027
Mutane sama da dubu goma sha daya ne suka kalla a lokacin hada wannan bincike yayin da sama da mutane dari da tamanin sukai shares.
Shima wani shafin na Facebook mai suna Grema Karagama ya wallafa bidiyon (archived here) ranar 29/12/2024 inda yake ikirarin cewa “ANOTHER ONE:💥💥💥 Ashe da gaske dai Sojojin Faransa sun shigo NIGERIA 😱😭

Haka shima wani shafi mai suna Usman Aljabbari Algwambawi ya wallafa wannan bidiyo ranar 27/12/2024 inda ya rubuta cewa “ Innalillahi wanna ilayihi rajiuna jama ar arewa mu qara Adu a sojojin faransa sun sigo arewa ccin Najeriya 😭😭

Shima wani wani shafi mai suna Hashim Danbala ya wallafa bidiyon ranar  (archived here) 28/12/2024 inda ya rubuta cewa “ Ashe da gaske dai Sojojin Faransa sun shigo NIGERIA 😢🥸

Bincike:

Da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta sanya bidiyon a wata manhaja ta gano cewa tsohon bidiyo ne da kafar dillancin labarai ta AP ta dauka kuma ya fara shiga yanar gizo ne tun a shekarar 2013 yayin da sojoji harda na Najeriya suka  sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Senou dake Bamako domin zuwa aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali.
Sojan Najeriya da aka gani yana magana a bidiyon dai Birgediya Janar Sa’ad Hanafi Abubakar mai ritaya ne wanda ya bar aikin soji tun shekarar 2016.
Haka zalika cikin jawabin sojin kasar Faransa a cikin bidiyo inda masana harshen Faransanci suka fassarawa Alkalanci anji yana cewa “akwai sojin Najeriya 156, sojin kasar Togo 100, 25 daga kasar Benin kuma ana sa ran zuwan wasu 25 daga kasar ta Benin daran yau.

Sakamakon Bincike:

Bisa la’akari da cewa bidiyon ya haura shekara goma da dauka, haka zalika duk faya-fayen bidiyon  da aka dinga yadawa harda wanda Alkalanci tayi bincike kwanakin baya inda ta gano sojin Birtaniya ne. Yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin dake saman tsohon bidiyon karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Karanta wannan

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar