Tun bayan samun saukin farashin man fetur daga matatar man Dangote dama kamfanin NNPCL ake samun labarai iri-iri harda na ƙarya.
Batu:
Wani shafin Facebook mai suna Taskira – H Online Tv ya wallafa wani iƙirari (archived here) a ranar 4/1/2025 inda yace; “YANZU YANZU: litar Man fetur zata koma Naira (500) nan Nada jimawa Ba, Dangote.”

Wani shafin Facebook mai suna Wakiliya a ranar (archived here) 3/1/2025 ya wallafa cewa “YANZU YANZU: litar Man fetur zata koma Naira (500) nan Nada jimawa Ba, Dangote.”

Bincike:
Kafar bindiddigi da bincike ta tuntubi mai magana da yawun rukunin kamfanin Dangote Anthony Chiejina inda yace “wannan labari karya ne. Tabbas mun fitar da sanarwar sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanoni kan man fetur, amma cewa munce farashin man fetur zai koma Naira dari biyar nan bada dadewa ba, karya ne.”
Haka zalika kafar bindiddigi ta Alkalanci ta duba kafafen yada labarai bata samu wannan labari ba a sahihan gidajen jaridu.
Sakamakon bincike:
La’akari da bayanin mai magana da yawun rukunin kamfanin Dangote daya karyata wannan labari, da kuma kasa samun wata sahihiyar kafar yada labarai data rawaito wannan labari, yasa kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan iƙirari ƙarya ne.
Labarai masu alaka: