Ranar farko ta shekarar 2025 wasu sun fara da yada ikirarin karya kan watan Janairun shekarar.
Batu:
Wani shafin Facebook mai suna Hussaini Lawan Roni ya wallafa wani ikirari a ranar 1/1/2025 inda yake cewa “ Bayan shafe shekaru 823 a Tarihi ba a samu irin wannan ba sai a wannnan shekarar ta 2025 Musulmai za su yi Sallar Juma’a sau 5 cikin Wata ɗaya. Wato cikin watan farako na Shekarar 2025. Allah buwayi gagara Misali.”

Shima wani shafin na Facebook mai suna Basiru A Shu’aibu ya wallafa wannan ikirari a ranar ta 1/1/2025 inda ya rubuta cewa “Bayan shafe shekaru 823 a Tarihi ba a samu irin wannan ba sai a wannnan shekarar ta 2025 Musulmai za su yi Sallar Juma’a sau 5 cikin Wata ɗaya. Wato cikin watan farako na Shekarar 2025. Allah buwayi gagara Misali.”
((https://www.facebook.com/share/p/14aB7aq862/?)) wanna wallafa dai ta sami shares sama da goma cikin awanni biyu da wallafawa.

Bincike:
Da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta duba tsoffin kalandun kwanan wata ta gano cewa, anyi ranakun Juma’a biyar a watan Janairun 2021. Wanda ranakun Juma’a biyar din suka kama a 1/1/2021, 8/1/2021, 15/1/2021, 22/1/2021 da 29/1/2021.
Shekarar 2020
Sannan shekarar 2020 ma an sami ranakun Juma’a biyar a wantan Janairun wannan shekara inda ranakun suka zama; 3/1/2020, 3/1/2020, 17/1/2020, 24/1/2020, 31/1/2020.
Shekarar 2016
Itama shekarar 2016 an sami ranakun Juma’a biyar a watan Janairun ta wanda suka fada, 1/1/2016, 8/1/2016, 15/1/2016, 22/1/2016 da 29/1/2016.
Sakamakon bincike:
Bisa samun shekarun baya-bayan nan na 2021, 2020, 2016 wanda suke kasa da shekaru goma da suka gabata da aka sami ranakun Juma’a biyar a cikin su, wanda kuma musulmai kanyi sallar Juma’a yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannna ikirari na shekaru 823 ba’a sami watan Janairu da Muslimai sukai sallar Juma’a biyar a ciki ba karya ne.