Wani bidiyo da aka wallafa a kafar sada zumunta ta Facebook inda ciki akai ikirarin kanzan kurege ko kuma ace shaci fadi wanda a turance ake kira myth dangane da Jemage.
Batu:
Wani shafin Facebook mai suna Chizo 1 germany ya wallafa wani faifan bidiyo (archived here) mai tsawon mintuna uku da sakan talatin da takwas a ranar 29/12/2024 inda ciki mai magana yayi ikirarin cewa Jemage ta baki yake hauhuwa. “Jemage ba tsuntsu bane kamar sauran tsuntsaye, shi Sam ba tsuntsu bane kamar tsuntsaye saboda ta baki yake haihuwa, babu tsuntsun dake haihuwa ta baki sai Jemage.”
Cikin awanni goma sha tara da wallafa wa bidiyon ya sami mutane sama da dubu goma sha bakwai da suka kalla, sama da mutane dari uku sun tofa albarkacin baki wato comments da kuma shares sama da dari biyu da goma.
Bincike:
Hukumar kare bacewar Jemagu a duniya ta wallafa cikakkiyar makala kan haihuwa da rayuwar Jemagu an sanyawa makalar suna “gano duniyar jariran Jemagu” cikin wannan makala dai an bayyana cewa Jemagu na haihuwa ta duburar su ne bata baki ba yayin da wacce ke taimakawa mai jegon wajen sanya jaririn da aka haifa zuwa Idan kan nono yake domin sha. Galibi kuma suna haihuwa cikin gungu ne wato masu ciki da yawa su taru su haihu lokaci guda.
Haka zalika akwai wani kundin bincike na masana dabbobin daji wato zoologist ya bayyana yadda Jemagu ke haihuwa da kuma yadda akwai unguwar zoma cikin jemagu dake taimakawa maijego wajen haihuwa.
Iya binciken masana dabbobi da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta karanta babu inda aka rawaito cewa akwai wani irin jinsin Jemage dake haihuwa ta baki.
Sakamakon bincike:
Binciken masana dabbobi musamman wadanda suka maida hankali kan jemage yaci karo da wancan ikirari na cewa Jemagu na haihuwa ta baki ne inda binciken ya fadi yadda suke haihuwa ta duburarar su, hakan yasa kafar bindiddigi ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wancan ikirari labarin kanzon kurege ne ko ace shaci fadi wato myth a turance don haka karya ne.