Tun bayan sabon zarge-zarge da gwamnatin kasar Nijar tawa gwamnatin Najeriya kan samar da sansanin sojin Faransa a wani yanki na arewacin Najeriya aka kara samun karuwar ikiraran karya a kafafafen sada zamunta.
Batu:
Wani shafin Facebook mai suna IG Wala ya
wallafa tsohon wani (archived
here) bidiyo ranar 27/12/2024 dake nuna sojin Najeriya dana Faransa suna kwasar kaya daga jirgin sama inda ana iya ganin jirgin sojin Najeriya a bidiyon wanda ya rubuta cewa “
Wadanne ‘yan gudun hijira ne wadannan masu kama da sojojin Faransa a Nigeria?😎 #Bamayi2027”
Mutane sama da dubu goma sha daya ne suka kalla a lokacin hada wannan bincike yayin da sama da mutane dari da tamanin sukai shares.
Shima wani shafin na Facebook mai suna Grema Karagama ya
wallafa bidiyon (archived
here) ranar 29/12/2024 inda yake ikirarin cewa “
ANOTHER ONE:💥💥💥 Ashe da gaske dai Sojojin Faransa sun shigo NIGERIA 😱😭”
Haka shima wani shafi mai suna Usman Aljabbari Algwambawi ya wallafa wannan bidiyo ranar 27/12/2024 inda ya rubuta cewa “ Innalillahi wanna ilayihi rajiuna jama ar arewa mu qara Adu a sojojin faransa sun sigo arewa ccin Najeriya 😭😭”
Shima wani wani shafi mai suna Hashim Danbala ya
wallafa bidiyon ranar (archived
here) 28/12/2024 inda ya rubuta cewa “
Ashe da gaske dai Sojojin Faransa sun shigo NIGERIA 😢🥸”
Bincike:
Da kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta sanya bidiyon a wata manhaja ta gano cewa tsohon bidiyo ne da kafar dillancin labarai ta AP ta dauka kuma ya fara shiga yanar gizo ne tun a shekarar 2013 yayin da sojoji harda na Najeriya suka sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Senou dake Bamako domin zuwa aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali.
Sojan Najeriya da aka gani yana magana a bidiyon dai Birgediya Janar Sa’ad Hanafi Abubakar mai ritaya ne wanda ya bar aikin soji tun shekarar 2016.
Haka zalika cikin jawabin sojin kasar Faransa a cikin bidiyo inda masana harshen Faransanci suka fassarawa Alkalanci anji yana cewa “akwai sojin Najeriya 156, sojin kasar Togo 100, 25 daga kasar Benin kuma ana sa ran zuwan wasu 25 daga kasar ta Benin daran yau.”
Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari da cewa bidiyon ya haura shekara goma da dauka, haka zalika duk faya-fayen bidiyon da aka dinga yadawa harda wanda Alkalanci tayi bincike kwanakin baya inda ta gano sojin Birtaniya ne. Yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin dake saman tsohon bidiyon karya ne.
Labarai masu alaka: