BindiddigiKo Sojojin Faransa Sun Iso Najeriya?

Ko Sojojin Faransa Sun Iso Najeriya?

-

Kome yasa ake cigaba da yada labaran karya kan kasar Faransa a Najeriya bayan wasu kasashe sun bukaci sojojinsu su fice?

Batu:

Akwai wani shafin Facebook mai suna Usman Yusuf Bala ya wallafa wani bidiyo dake nuna wani sojan Najeriya na magana kan yaki da ‘yan Boko Haram a gefensa akwai sojoji turawa wanda a saman bidiyon ya rubuta cewa “ Nan a France ne ko a Nigeria ne Sundai karaso kenan.”
Wannan bidiyo dai ya sami mutane sama da dubu goma sha uku da suka kalla a kasa da awanni 24 da wallafa shi.
Akwai dai ikirari da ake yadawa a harshen turanci na cewa sojojin Faransa sun iso Najeriya domin kafa sansani bayan korarsu wasu kasashe sukayi.

Bincike:

Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta dauki hoton wani sashe na bidiyo tare da binciken lokacin da aka dauka da kuma suwaye turawan?
Binciken ya nuna cewa turawan dake bidiyon na Ingila ne bana Faransa ba. Haka zalika baturen dake gefen sojin Najeriya ba wani bane face Kanal Martin Leach wanda sananne ne a tawagar horaswa ta sojin Birtaniya, ya kuma zama babban wanda ya karfafa alakar soji tsakanin sojojin Najeriya da Birtaniya.
Ko a watan Oktoban wannan shekara sojin da aka gani a bidiyon wato Kanal Leach ya kawowa Najeriya tallafin makaman yaki da suka kai kusan biliyan daya domin yaki da ‘yan Boko Haram.
Shalkwatar dakarun tsaro ta Operation Hadin kai itama ta musunta cewa akwai sojojin Faransa inda tace bidiyon da aka gani ba kowa bane face Birgediya Janar Haruna yake magana da ‘yan jaridu yayin da suka karbi tallafin makamai daga sojojin Burtaniya a watan Oktoba.

Sakamakon Bincike:

Kasancewar wannan bidiyo tsohon bidiyo ne kuma turawan da aka gani a bidiyon sojojin Burtaniya ne ba na Faransa ba kamar yadda ake ikirarin. Wannan yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari na cewa sojojin Faransa sun iso Najeriya karya ne.
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar