Yayin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yiwa majalisar zartarwar jihar garambawul tare da korar wasu ‘yan majalisar zartarwa wanda ya hada da sakataren gwamnatin jihar Bappa Bichi an sami labaran karya da mutane ke yadawa wanda ya hada harda wasu gidajen radiyo a jihar.
Batu:
Wani shafi mai suna Daily Post ya wallafa labarin cewa “Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Ya Ziyarci Shekaru”.
Sannan wani shafin Facebook mai suna Ammasco Radio yayi ikirarin cewa tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Abdullahi Bappa Bichi ya kaiwa tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim shekarau ziyara.

Bincike:
Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi Sule Ya’u Sule mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekaru inda ya fadawa Alkalanci cewa “hoton da ake yadawa tsohon hotone lokacin da shi Bappa Bichi ya kaiwa Shekarau jaje yayin da akai gobara a gidansa.” Ya kara da cewa “Idan akwai wani abu kamar haka (ganawa) tabbas bazai tafi ba tare da an sani ba.”
Haka zalika Alkalanci ta tuntubi bangaren Bappa Bichi inda makusantansa suka bayyana cewa hoton da ake yadawa tsohon hotone kuma tsohon sakataren gwamnatin bai ziyarci tsohon gwamnan ba.
Sakamakon Bincike:
Bisa samun tabbacin cewa hoton da ake yadawa tsoho ne kuma masu magana da yawun Bappa Bichi da Ibrahim Shekaru sun karyata faruwar ganawa tsakanin mutanen biyu tun bayan korar Bappa Bichi. Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.