BindiddigiShin Sanata Barau Ne Ya Jagoranci Wucewar Kudirin Dokar...

Shin Sanata Barau Ne Ya Jagoranci Wucewar Kudirin Dokar Haraji Zuwa Karatu Na Biyu?

-

Kudirin haraji da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gabatarwa majalisun tarayyar Najeriya ya janyo zazzafan muhawara da suka a tsakanin ‘yan siyasa, talakawa dama malaman addini.
Wannan kudiri doka wanda ya haɗa da sashi na 77, wanda yake bukatar sake fasalin tsarin harajin Najeriya. Sai dai wasu masana na ganin aiwatar da wannan kuduri na ɗauke da matsaloli masu yawa game da tasirin tattalin arziki ga arawacin Najeriya, dama kudu maso gabashin Najeriya.
Kamar dai wasu batutuwa shima wannan batu yazo da kalamai da ikirari na karya da kuma wasu na kauda hankulan mutane.

Batu:

Babban abinda yafi fitowa fili kuma yafi yaduwa a kafafen yada labarai dama kafafen sada zumunta shine faifan bidiyon da ya fito inda mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril ke cacar baki da Sanata Ali Ndume a zauran majalisar dattawa yayin kwamitin kudirin dokar suka shiga zauran majalisar dan yin jawabi kan abinda kudirin dokar ke dauke dashi.
Bayan wannan bidiyo da kuma labaran cewa kudirin ya wuce zuwa karatu na biyu ranar alhamis wasu suka dinga yada cewa Sanata Barau Jibrin ne ya jagoranci zaman majalisar da aka amince kudirin dokar ya tafi zuwa karatu na biyu.
Wani shafin Facebook mai suna Mikiya ya wallafa ikirarin cewa Sanata Barau ne ya jagoranci zaman majalisar dattawa ranar da kudirin dokar haraji ya wuce zuwa karatu na biyu. “ Sanata Barau Jibrin ne ya Jagorancin Majalisar dattijan wajen Amincewar majalisar dattijai da ake ta cece-kuce kan kudirin sake fasalin haraji da ya wuce karatu na biyu wanda ya haifar da cece-ku-ce, musamman dangane da rawar da Sanata Barau Jibrin ya taka a harkar.”
Wannan wallafa (adana bayanai a NAN) dai ta sami mutane sama da dari biyar wadanda suka tofa albarkacin baki wato comment yayin da sama da mutane dari biyu suka kara yadawa wato shares.
Hoton ikirarin da wani mai suna Mikya ya wallafa.
Hoton ikirarin da wani mai suna Mikya ya wallafa.
Shima wani mai suna Mustpha Isa Barau  a shafin Facebook ya wallafa ikirarin cewa  (adana a NAN)Sanata Barau Jibrin ne ya Jagorancin Majalisar dattijan wajen Amincewar majalisar dattijai da ake ta cece-kuce kan kudirin sake fasalin haraji da ya wuce karatu na biyu wanda ya haifar da cece-ku-ce, musamman dangane da rawar da Sanata Barau Jibrin ya taka a harkar. Wasu da dama na kallon abin da ya yi a matsayin cin amana, wanda hakan ke kara nuna rashin damuwarsa kan yadda ya jajirce wajen biyan bukatun kansa a maimakon bukatun al’ummar Arewacin Najeriya da ma talakawan kasar baki daya.”
Hoton ikirarin da wani mai suna Mustapha Isah Barau ya wallafa.
Hoton ikirarin da wani mai suna Mustapha Isah Barau ya wallafa.

Bincike:

Da kafar bindiddigi ta Alkalanci ta binciki wancan ikirari ta gano cewa a ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba, 2024 a zaman majalisar dattawan anyi muhawara kan batun kudirin yiwa dokar haraji kwaskwarima wanda aka yada zaman kai tsaye a shafin YouTube dama gidan Talabijin na NTA. A ranar dai shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ne ya jagoranci zaman majalisar wanda a wannan ranar ce kudirin ya wuce zuwa karatu na biyu.
Zaman majalisar dattawan da aka yada a shafin majalisa.
Zaman majalisar dattawan da aka yada a shafin majalisa.

Sakamakon Bincike:

Bisa samun zaman majalisar dattawan da aka yada a shafin majalisar na YouTube da kuma NTA ya tabbatar da cewa ba Sanata Barau bane ya zauna ranar da kudirin ya wuce karatu na biyu don haka kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta yanke hukunci cewa wancan ikirari karya ne.

Shin Karatu Na Biyu Na Nufin Majalisa Ta Amince Da Kudurin Dokar Kenan?

Bayan labarin cewa kudirin dokar harajin ta wuce zuwa karatu na biyu, wannan ya haddasa rubuce-rubuce da kuma tattaunawa a kafafen yada labarai dama na sada zumunta inda kafar Alkalanci taci karo da zantawa na kai tsaye sama da goma a shafin Tiktok da wasu da dama a shafin X (Twitter).
Zantuttukan da dama dai na bada karfi kan cewa tunda kudurin ya wuce zuwa karatu na biyu na nufin cewa majalisar dattawan ta aminta da kudirin dokar.
Akwai dai malaman addini da dama da sukai hudubar Juma’a kan wannan batu misali shahararren malamin nan na Sokoto Farfesa Mansur Ibrahim yayi huduba inda yayi ikirarin cewa ana boye tare da gaggawar a amince da kudirin dokar ba tare da an bayyana abinda ke cikin kudirin ga mutane su sani ba.

Bincike:

Da dama daga Sanatocin dai sun bayyana cewa basu da isasshen ilimi da bayani kan wannan kudirin doka.
Sanata Babangida Hussaini daga jihar Jigawa yace wuce war kudiri zuwa karatu na biyu baya nufin aminta da kudiri fyace kara bincike da tattaunawa akan kudirin.
Haka zalika yace akwai zaman masu ruwa da tsaki wato public hearing inda anan ne duk masu ruwa da tsaki ke haduwa su tattauna kan kudirin tare da gabatar da sakamako akan kudirin.
Sanatocin arewa sun gana kuma sun tattauna kan wannan kudiri babu yadda za’ayi mu amince da wani kudirin doka dazai cutar da mutanen mu. Akwai matakai biyu zuwa uku da dole kudirin doka yabi kafin ya zama doka mai zaman kanta. A daina tada jijiyar wuya, zamuyi abunda ya dace.
Haka zalika bincike ya nuna cewa mafi akasarin kudirin doka da ake gabatarwa a majalisar dattawa kan wuce zuwa karatu na biyu wanda daga nan take tafiya zuwa kwamiti sai kuma zaman masu ruwa da tsaki na jin ra’ayoyin mutane wato public hearing a turance wanda ba kowacce bace take wuce wannan mataki har majalisa ta aminta da ita ta zama doka.

Sakamakon Bincike:

Bisa yanayin tsarin wucewar kudirin doka na majalisar dattawa ya nuna cewa don kudiri ya shiga karatu na biyu ba shi ke nuna cewa majalisa ta amince da kudirin ba, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari na cewa majalisa ta amince da kudirin dokar haraji a matsayin karya ne.

Labarai masu alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Karanta wannan

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar