Alakar kasar Nijar da kungiyoyin kasa da kasa dai ta fara samun matsala ne tun bayan juyin mulki, wanda aka dinga samun ikirari da labaran karya kan wasu matakan kasar ta Nijar dama su kungiyoyin.
Batu:
Wani shafin kafar sadarwa ta Facebook mai suna Damagaran Post ya wallafa wani ikirari na cewa (Adana bayanai a NAN) “kasar Nijar ta kori jakadan tarayyar turai daga kasar.”
Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta fara da tuntubar kungiyar tarayya turai inda ta Sami sanarwar da tarayyar turan ta fitar a harshen Faransanci take cewa ta yiwa jakadan nata kiranye ne don jin bahasi.
Sanarwar tace; “Tarayyar turai dai ta sami sanarwar da gwamnatin Nijar ta fitar da take kalubalantar yadda wakilan tarayyar turai a kasar suka raba kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa. Tarayyar turai bata gamsu da zarge-zarge da rashin jituwar da gwamnatin Nijar take yiwa wakilan EU din ba. Wannan dalili yasa EU ta bukaci jakadanta dake Niamey daya je babban ofishin EU dake birnin Brussels domin jin bahasi.”
Ma’aikatar harkokin wajen Nijar dai na zargin EU da raba kayayyakin agaji ba tare da tuntuba ko sahalewar gwamnatin kasar ba.
To sai dai EU tace a yayin da kasar ta Nijar ke fama da matsaloli tana da kudirin cigaba da bada tallafi ga ‘yan kasar musamman ta amfani da hukumomin majalisar dinkin duniya dama kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa.
Ma’aikatar harkokin wajen ta Nijar dai dama sun bukaci kungiyar ta EU data canza jakadan bisa zarginsa da yin katsalandan a harkokin cikin gidan kasar.
To sai dai EU ta musanta wancan zargi inda tace bazata bari a siyasantar da kayan agaji da take bayarwa ba.
Sakamakon Bincike:
Binciken kafar bindiddigi na Alkalanci dai ya rasa samo inda hukumomin kasar suka bukaci jakadan daya bar kasar wato sun koreshi fyace bukatar a canza musu shi. Wannan yasa wannan ikirari na Damagaram Post ya zama karya ne.