A ranar larabe ce dai wata kotun tarayya a Abuja ta baiwa babban bankin kasar CBN da ofishin akanta janar na kasar da kada su baiwa gwamna jihar Ribas kudin wata a ake baiwa jihohi.
Batu:
Wani labari dai yana yadu matuka a harshen turanci wanda wasu suka fara fassarashi zuwa Hausa Ina labarin ke cewa “Gwamnan jihar Ribas Sim Fubura ya rufe kamfanin NNPC da duk kamfanonin hakar mai a jihar inda ya ayyana cewa Idan akace babu kudin jihar daga gwamnatin tarayya to babu hakar mai…”
Labarin ya kara da cewa “…Mintuna kadan da wannan ayyanawa Najeriya ta sauka daga matsayin kasa ta hudu mai hako mai zuwa kasa ta ashirin da hudu.
Wani mai suna Manir Ahmad a shafinsa na Facebook ya wallafa wannan labari inda yake cewa “Alaji Fubara ya tsaya da kafafuwan sa fa.”

Sannan an sami wasu da suka yada irin wannan labari da salo daban-daban.

Bincike:
Binciken Alkalanci ya gano ya tuntubi kwamishinan yada labaran jihar Warisenibo Johnson inda yace labarin karya ne, gwamnatin Ribas mai mutunta doka ce.
Sannan binciken Alkalanci ya gano cewa Najeriya ba itace kasa ta hudu dake samar Ko fitar da man fetur ba,balle har ta sauka daga wannan mataki. rahoton hukumar makamashi na duniya wato IEA ya nuna cewa a bangaren samar da danyen mai Najeriya ce kasa ta 2 a Afrika a shekarar 2022.
Yayin da ta zama kasa ta goma sha shida a duniya.
Sakamakon Bincike:
Bisa wannan bincike Alkalanci ya yanke hukuncin cewa wannan labari karya ne wato false a turance.