BindiddigiShin Jami’ar Abuja Na Yin Kwasa-Kwasai Kyauta?

Shin Jami’ar Abuja Na Yin Kwasa-Kwasai Kyauta?

-

Tun lokacin matsalar cutar Covid-19 jami’o’i a fadin Najeriya suka fara karfafa karatu ta yanar gizo wato online. Duk da cewa akwai jami’ar NOUN da ta dade tana gudanar da karatu ta yanar gizo ga dalibanta. Hakan bai hana sauran jami’o’i suma samar tare da karfafa wannan bangare ba.

Batu:

Akwai wani sako dake yawo a shafin Facebook wanda ke nuna cewa jami’ar Abuja tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi na samar da kwasa-kwasai ta yanar gizo kyauta ga al’ummar kasar.
Wani shafin Facebook mai suna Lifeserviced ya wallafa wannan sanarwa  (archived here) kamar haka:
“Darussan Fasaha na Kan layi Kyauta
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da hadin gwiwar Jami’ar Abuja na samar da kwasa-kwasan kan layi kyauta ga al’umma a fadin kasar nan 18-30 shekaru 31-50 shekaru 51-70 shekaru”

Mutane da dama dai sun tofa albarkacin bakin su a wannan wallafa inda suke neman yadda zasuyi rijista. Yayin da wasu da dama suke yada wato shares.

An sami irin wannan wallafa da take cewa jami’ar Najeriya dake Nsukka itama tana samar da kwasa-kwasai kyauta ta yanar gizo.

Bincike:

Alkalanci ya binciki wannan wallafa wanda da farko dai Hausar da akai amfani da ita ba mai kyau bace domin an fassara “online” a matsayin “kan layi” sannan kuma anyi amfani da hoton tsohon shugaban jami’ar Farfesa Abdulrasheed Na’Allah mai makon Shugabar riko ta jami’ar wato Farfesa Aisha Maikudi.
Sannan Alkalanci ya tuntubi mai magana da yawun jami’ar Abuja din Dr. Habib Yakoob inda yace “Sanarwar karya ce, kuma jami’ar Abuja bata yin wani kwas na yanar gizo kyauta.

Sakamakon Bincike:

Binciken Alkalanci ya gano cewa wannan sanarwa karyace da kuma kokarin zambatar mutane da wasu ke kokarin yi.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar