A satin daya gabata dai wasu bankuna a Najeriya sun sami tangardar network saboda wasu dalilai wanda yasa ‘yan kasar da dama kasa turo ko cirar kudi na ‘yan kwanaki.
Ikirari:
Akwai wani bidiyo mai tsawon mintuna 6 da sakan 47 wanda wani yake magana da harshen Hausa kuma yake ikirarin cewa kara bunkasa aikin network da bankuna keyi wato upgrade wani salone na fara cirewa mutane kudade da sunan tax basu sani ba.
Bidiyon dai ya sami (archived here) shares sama da dari biyar yayin da mutane sama da dubu talatin suka kalla.
Ga dai abubuwan daya fada daga sakan daya zuwa kusan mintuna biyu na bidiyon;
“‘Yan arewa Idan baka san wannan ba TIN upgrade wanda banki sukeyi ba, dan Allah ku saurara kuji. Wannan upgrade wanda kuka ji cewa sati biyun da suka wuce zenith bank basu da network baku iya samun kudi ba ba kuyi komai ba ko? Yayi kamar kwana biyu ko uku ba network, last week UBA sukayi nasu suka haka ba’a sami network ba ko? Jiya GTBANK basu da network bansan Ko sun gyara ba domin Nima naje wajen anmin wannan ba network. Wannan upgrade da aka ce TIN upgrade to bari na gaya muku tax ne, kudinku za’a dinga cirewa daga account, akwai lokacin da na taba muku magana nace lokaci yana zuwa za’a fara cire kudin ku a banki ba’a sani ba a gaya muku tax ne baku sani ba waye zaku tambaya babu. Kuma sanatoci ne sukai approving wannan abun an rigada an tura abin nan, an tura shi tuntuni suna kai akai approving. Yanzu an fara ciccire wannan tax din. Kudinka yana ajiye a account Ko dubu daya za’a cire wannan tax din tax normally ya kamata kamfanoni suke biya, karamin kamfani ne koma yane inda kamfani ne kafin ka bude company account a banki dole sai kana da TIN number. Yanzu kowanne mutum zai sami nashi in ka samu shikenan basu neman a wannan dinka ah permission dinka, su cire kudin zasu cire….
Bincike:
Alkalanci ta fara duba shafukan wasu daga cikin bankunan da aka sami wannan tangarda cikin a inda muka fara da bankin GTBANK wanda cikin sanarwar da bankin ya fitar a shafinsa dama shafin Facebook ya bayyanawa abokan huldarsa cewa zai yi wannan aiki da suka kira upgrade domin karfafa manhaja tare da ganin an sami sauki da saurin huldar hada-hadar kudi musamman a fannin hulda ta yanar gizo wato online banking Ko transactions.
Mun tuntubi wasu da suka amfani da bankin na GTbank misali Ahmad Muhammad yace tun kafin a sami wannan tangarda tabbas bankin sun turamin da sakon email suka sanar dani kuma bayan sun kammala upgrade din nan ma sun turamin email na samun nasarar upgrade din.
Haka shima bankin Zenith a cikin shafin na Facebook ya wallafa sanarwar bunkasa naurar ayyuka daya kira upgrade din (IT infrastructure) inda yace upgrade din ya zama dole domin abokan hulda suyi amfani da manhajar bankin dama sauran huldodi cikin sauki da kuma sauri.
Alkalanci har ila yau ta bincika ikirarin amfani da upgrade din wajen cirar haraji wato tax, wanda muka fara duba iya kudaden da babban banki ya sahalewa bankuna su cira daga asusun yan kasar kodai Idan sunyiwa mai asusu aiki ko kuma cikin abinda doka ta bada dama.
Kowanne dan kasa dai yana biyan haraji kodai kai tsaye a cira daga albashin sa ko kuma harajin Kan abubuwan amfani ko ci wato VAT.
A iya binciken da mukayi a shafukan babban bankin Najeriya wato CBN dama shafin hukumar karbar haraji ta Najeriya wato FIRS dai babu wani sabon haraji da aka baiwa bankuna su dinga cira daga asusun mutane haka siddan.
Sakamakon Bincike:
Sakamakon binciken Alkalanci ya nuna cewa ikirarin da akayi a wannan bidiyo dai karya ne domin rashin samun hujja daga shafukan bankuna, CBN dama hukumar FIRS.
Zaku iya duba iya abubuwan da bankuna aka sahale musu su cira wato charges a wadanna links guda biyu a kasa.
Reference links: