Shin Hoton Rashin Lafiyar Tinubu Gaskiya Ne?
Akwai dai mutane da dama a Najeriya da suka wallafa wani hoto a Facebook dama yin karamin bidiyo a YouTube dake nuna shugaban Najeriya Bola Tinubu kwance a gadon asibiti.
A cewar wadanda suka wallafa hotunan shugaba Tinubu na kwance rai a hannun Allah.
Daya daga cikin wanda suka wallafa hoton a Facebook mai suna Hon M Gwabba (archived here) yace “ Munaneman Baran Addu’a daga gareku,sakamakon Maigirma Shugaban Kasar Nigeria.
(Asiwaju Bola Ahmad Tinubu)baida lafiya.Wani Fata Zakuyimasa???”

Haka zalika wannan hoto an yadashi a YouTube (archived here) inda ake ikirarin cewa Tinubun na kwance a asibiti.
Hoton dai da ake yadawa ba na shugaban Najeriya bane wato dai anyi amfani da fasahar gyara hoto na photoshop aka cire fuskar asalin maras lafiyar aka sanya fuskar shugaban Tinubu domin a nuna cewa baida lafiya.
Binciken Alkalanci dai ya nuna cewa wannan hoto dai karya ne.