Hukunci: Ƙarya ne
Bisa la'akari da bayanan da shugaban ƙasar Senegal Bassírou Diomaye Diakhar Faye ya yi da wanda shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron yayi wanda ba kalamai iri ɗaya bane. Sannan babu wata sahihiyar gidan jarida ko yaɗa labarai data rawaito wannan labari duk da girman sa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukunci cewa iƙirarin cewa shugaban Senegal ya karbi jawabin shugaban Faransa yayi jawabi a taron na majalisar dinkin duniya ƙarye ne.
Wani shafin Facebook mai suna Nijer Hausa 24 ya wallafa wani iƙirari dake cewa shugaban ƙasar Senegal Bassírou Diomaye Diakhar Faye ya karanta jawabin shugaban Faransa Emmanuel Macron a taron shekara-shekara na majalisar ɗinkin duniya UNGA.
Shafin yayi rubutu kamar haka:
Shugaban Senegal Ya Karɓi Jawabin Da Macron Ya Rubuta a Majalisar Dinkin Duniya?
shugaban Senegal, Béchir Diouma Fay ya bayyana a gaban duniya da wani jawabi da ya janyo ce-ce-ku-ce. A cewar rahotanni, shugaban ya karanta jawabi da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya rubuta, maimakon ya gabatar da nasa.
Abin da ya fi jan hankali shi ne yadda ya buɗe jawabin da yabon Faransa, ba tare da taɓo manyan matsalolin da ke addabar nahiyar Afrika ba kamar ta’addanci, talauci, cin hanci da rashin ‘yancin tattalin arziki
Shin hakan ba cin mutunci bane ga Senegal da duk nahiyar Afrika?

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba bayanan na shugaban Senegal a shafin YouTube na majalisar ɗinkin duniya, inda ta saurara tare da ganin yadda abin ya faru a zauren taron.

To sai dai a bidiyo babu wani abu daya nuna hakan domin kuwa jawabin na shugaban ƙasar ta Senegal ya sha bambam da na shugaban ƙasar Faransa. Kuma ba a rana ɗaya suka gabatar da jawabi ba.
Haka zalika an ɗan sami tsauko na daƙiƙu kafin yayi jawabi saboda tasgaro da aka samu daga masu tsara ko nuna jawabai daga na’urar dake gaban shugaban na Senegal.
Alkalanci ta tuntubi wata ƴar jaridar ƙasar Senegal da ta halarci zaman taron na majalisar ɗinkin duniya mai suna Sofia Ba inda tace bayanin cewa shugaban na Senegal ya karanta jawabin shugaban Faransa ƙarya ce tsagoranta.
Sakamakon bincike:
Bisa la’akari da bayanan da shugaban ƙasar Senegal Bassírou Diomaye Diakhar Faye ya yi da wanda shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron yayi wanda ba kalamai iri ɗaya bane. Sannan babu wata sahihiyar gidan jarida ko yaɗa labarai data rawaito wannan labari duk da girman sa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukunci cewa iƙirarin cewa shugaban Senegal ya karbi jawabin shugaban Faransa yayi jawabi a taron na majalisar dinkin duniya ƙarye ne.
