BindiddigiƘarya ne: Shugaban Senegal bai karanta jawabin shugaban Faransa...

Ƙarya ne: Shugaban Senegal bai karanta jawabin shugaban Faransa ba

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa la'akari da bayanan da shugaban ƙasar Senegal Bassírou Diomaye Diakhar Faye ya yi da wanda shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron yayi wanda ba kalamai iri ɗaya bane. Sannan babu wata sahihiyar gidan jarida ko yaɗa labarai data rawaito wannan labari duk da girman sa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukunci cewa iƙirarin cewa shugaban Senegal ya karbi jawabin shugaban Faransa yayi jawabi a taron na majalisar dinkin duniya ƙarye ne.

Wani shafin Facebook mai suna Nijer Hausa 24 ya wallafa wani iƙirari dake cewa shugaban ƙasar Senegal Bassírou Diomaye Diakhar Faye ya karanta jawabin shugaban Faransa Emmanuel Macron a taron shekara-shekara na majalisar ɗinkin duniya UNGA.

Shafin yayi rubutu kamar haka:
Shugaban Senegal Ya Karɓi Jawabin Da Macron Ya Rubuta a Majalisar Dinkin Duniya?
 shugaban Senegal, Béchir Diouma Fay ya bayyana a gaban duniya da wani jawabi da ya janyo ce-ce-ku-ce. A cewar rahotanni, shugaban ya karanta jawabi da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya rubuta, maimakon ya gabatar da nasa.
Abin da ya fi jan hankali shi ne yadda ya buɗe jawabin da yabon Faransa, ba tare da taɓo manyan matsalolin da ke addabar nahiyar Afrika ba  kamar ta’addanci, talauci, cin hanci da rashin ‘yancin tattalin arziki
 
Shin hakan ba cin mutunci bane ga Senegal da duk nahiyar Afrika?
Labarin karya dake cigaba da yaduwa
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba bayanan na shugaban Senegal a shafin YouTube na majalisar ɗinkin duniya, inda ta saurara tare da ganin yadda abin ya faru a zauren taron.
Hoton shafin majalisar dinki duniya lokacin da shugaban Senegal ke jawabi
To sai dai a bidiyo babu wani abu daya nuna hakan domin kuwa jawabin na shugaban ƙasar ta Senegal ya sha bambam da na shugaban ƙasar Faransa. Kuma ba a rana ɗaya suka gabatar da jawabi ba.
Haka zalika an ɗan sami tsauko na daƙiƙu kafin yayi jawabi saboda tasgaro da aka samu daga masu tsara ko nuna jawabai daga na’urar dake gaban shugaban na Senegal.
Alkalanci ta tuntubi wata ƴar jaridar ƙasar Senegal da ta halarci zaman taron na majalisar ɗinkin duniya mai suna Sofia Ba inda tace bayanin cewa shugaban na Senegal ya karanta jawabin shugaban Faransa ƙarya ce tsagoranta.
Sakamakon bincike:
Bisa la’akari da bayanan da shugaban ƙasar Senegal Bassírou Diomaye Diakhar Faye ya yi da wanda shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron yayi wanda ba kalamai iri ɗaya bane. Sannan babu wata sahihiyar gidan jarida ko yaɗa labarai data rawaito wannan labari duk da girman sa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukunci cewa iƙirarin cewa shugaban Senegal ya karbi jawabin shugaban Faransa yayi jawabi a taron na majalisar dinkin duniya ƙarye ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar