Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun tabbacin cewa Nasiru Adamu El-Hikaya baya cikin waɗanda aka kora a shekarar 2018 bisa laifin karbar kuɗin da ya kai dala dubu biyar daga wani gwamna bayan hira dashi a ɗakin watsa labarai.
Haka zalika ganin cewa Nasiru Adamu El-Hikaya ya cigaba da tura rahotanni da kuma shiri a sashen Hausa na Amurka har zuwa watan da shugaban ƙasar ta Amurka Donald Trump ya bada umarnin dakatar da aikin VOA yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa Amurka ta kori Nasiru Adamu El-hikaya bisa zargin karbar cin hanci karya ne.
Akwai wani shafin Facebook mai suna Gimbiyar Hausa ya wallafa wani iƙirari kan cewa ta kori wani ɗan jaridar VOA mai suna Nasiru Adamu El-Hikaya saboda karbar cin hanci.
Iƙirarin kamar haka; “America basa Wasa da cin hanci jama’a, yadda kasar America ta kori wani ɗan jarida daga sashin Hausa na Voice of America wato VOA Hausa, mai suna Nasiru Adamu El-hikaya ɗan Fulani bisa tsargin karbar cin hanci na $5000.”
Wannan wallafa ta sami tofa albarkacin baki wato comments da dama yayin da wasu suka aminta da wannan iƙirarin tare da zagi, wasu kuma sun musunta hakan.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa Muryar Amurka VOA ta kori wasu ma’aikatan ta ne dake aiki a Washington DC, a shekarar 2018 bayan zargin karbar kuɗi daga hannun wani gwamna daga arewacin Najeriya.
Wannan kora wacce ta shafi iya waɗanda suke a can kuma suka yi aiki a ranar da abin ya faru ne.
Sashen Turanci na VOA ya wallafa wannan labari inda gidan jaridar Daily Trust shima ya rawaito wannan rahoto a shekarar ta 2018.
Binciken Alkalanci ya gano cewa Nasiru Adamu El-Hikaya bai taba aiki a Washington DC ba, ya kasance wakili ne na Muryar Amurka VOA a Abuja Najeriya na shekaru da dama.
Har ya zuwa watan da shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin dakatar da aikin dukkan sashen VOA a shekarar 2025, Nasiru Adamu El-Hikaya na turawa da rahoto.
Sakamakon bincike: