BindiddigiƘarya ne: Nasiru El-Hikaya baya cikin waɗanda VOA suka...

Ƙarya ne: Nasiru El-Hikaya baya cikin waɗanda VOA suka kora a shekarar 2018

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun tabbacin cewa Nasiru Adamu El-Hikaya baya cikin waɗanda aka kora a shekarar 2018 bisa laifin karbar kuɗin da ya kai dala dubu biyar daga wani gwamna bayan hira dashi a ɗakin watsa labarai. Haka zalika ganin cewa Nasiru Adamu El-Hikaya ya cigaba da tura rahotanni da kuma shiri a sashen Hausa na Amurka har zuwa watan da shugaban ƙasar ta Amurka Donald Trump ya bada umarnin dakatar da aikin VOA yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa Amurka ta kori Nasiru Adamu El-hikaya bisa zargin karbar cin hanci karya ne.
Akwai wani shafin Facebook mai suna Gimbiyar Hausa ya wallafa wani iƙirari kan cewa ta kori wani ɗan jaridar VOA mai suna Nasiru Adamu El-Hikaya saboda karbar cin hanci.
Iƙirarin kamar haka; “America basa Wasa da cin hanci jama’a, yadda kasar America ta kori wani ɗan jarida daga sashin Hausa na Voice of America wato VOA Hausa, mai suna Nasiru Adamu El-hikaya ɗan Fulani bisa tsargin karbar cin hanci na $5000.”
Wannan wallafa ta sami tofa albarkacin baki wato comments da dama yayin da wasu suka aminta da wannan iƙirarin tare da zagi, wasu kuma sun musunta hakan.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa Muryar Amurka VOA ta kori wasu ma’aikatan ta ne dake aiki a Washington DC, a shekarar 2018 bayan zargin karbar kuɗi daga hannun wani gwamna daga arewacin Najeriya.
Wannan kora wacce ta shafi iya waɗanda suke a can kuma suka yi aiki a ranar da abin ya faru ne.
Sashen Turanci na VOA ya wallafa wannan labari inda gidan jaridar Daily Trust shima ya rawaito wannan rahoto a shekarar ta 2018.
Binciken Alkalanci ya gano cewa Nasiru Adamu El-Hikaya bai taba aiki a Washington DC ba, ya kasance wakili ne na Muryar Amurka VOA a Abuja Najeriya na shekaru da dama.
Har ya zuwa watan da shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin dakatar da aikin dukkan sashen VOA a shekarar 2025, Nasiru Adamu El-Hikaya na turawa da rahoto.
Sakamakon bincike:
Bisa samun tabbacin cewa Nasiru Adamu El-Hikaya baya cikin waɗanda aka kora a shekarar 2018 bisa laifin karbar kuɗin da ya kai dala dubu biyar daga wani gwamna bayan hira dashi a ɗakin watsa labarai.
Haka zalika ganin cewa Nasiru Adamu El-Hikaya ya cigaba da tura rahotanni da kuma shiri a sashen Hausa na Amurka har zuwa watan da shugaban ƙasar ta Amurka Donald Trump ya bada umarnin dakatar da aikin VOA yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa Amurka ta kori Nasiru Adamu El-hikaya bisa zargin karbar cin hanci karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar