Hukunci: Ƙarya ne
Binciken Alkalanci ya kasa samun wani waje da kamfanin Meta ya bayyana cewa ya ba ƴan Najeriya wa'adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa ba. Sannan babu wani labari dake nuna cewa akwai haɗin gwiwa tsakanin Meta da gwamnatin Najeriya. Haka kuma babu inda Meta ya bayyana cewa yawan shafukan Facebook a Najeriya ya kai sama da miliyan 700. Bisa rashin samun sahihan bayanai daga a shafukan Meta da hukumomin gwamnatin Najeriya dangane da wannan iƙirarin yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ƙarya ne.
Hukumomi a Najeriya dai sun rufe ko ace nome dubunnan shafukan sada zumunta bisa zargin su da laifuka daban-daban.
Iƙirari:
Wasu shafukan facebook dai sun wallafa iƙirarin cewa kamfanin Meta wanda ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya baiwa ƴan Najeriya wa’adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa ko wasu ID da aka aminta dasu.
Wani shafin na Facebook mai suna APA Hausa ya wallafa iƙirarin kamar haka;
“Kamfanin Meta mamallakin shafukan sada zumunta na zamani mafiya girma a Duniya Facebook da Instagram, ya ba ƴan Najeriya wa’adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa, saboda akwai adadin accounts fiye da miliyan 700 a Najeriya wanda kuma illahirin ƴan ƙasar basu wuce miliyan 230 ba, Meta yace zai rufe duk wani account ɗin bogi.”

https://www.facebook.com/share/p/1FAK9B5JXj/?mibextid=wwXIfr
Wani shafin ma mai suna Giade post ya wallafa wannan iƙirarin.

Bincike:
Binciken Alkalanci ya duba shafukan kamfanin na Meta amma babu wannan labari.
Haka zalika mun duba shafukan hukumomin gwamnatin Najeriya irin su NITDA da NCC to amma babu wannan labari.
To sai dai kafar tantance labarai ta Alkalanci ta ga bayanan dake nuna cewa Facebook ba ya bukatar sunan ka ya dace da na National ID, Fasfo, ko katin tuki ko katin zabe don amfani da shafin.
Amma idan mutum yana son ayi verifying dinsa ko shafin mutum ya sami matsala (misali an rufe shi saboda taka doka), to za su bukaci ka tabbatar da kai ne mai shi ta hanyar ID.
Hakan dai na nufin ba dole bane sunan da ke Facebook ya yi dai-dai da na ID.
Haka zalika babu wata hadin gwiwa tsakanin Facebook da Gwamnatin Najeriya akan rufe shafuka.
Facebook kamfani ne mai zaman kansa. Ba ya aiki kai tsaye da gwamnati don rufe shafi sai idan akwai dalilan tsaro ko taka doka (kamar labaran karya, kutse, damfara, da sauransu).
Babu wata shaida dake nuna cewa Facebook ya goge ko nome miliyoyin shafuka saboda suna baiyi dai-dai da na ID ba.
Binciken Alkalanci ya gano cewa haka siddin Facebook ba zai goge shafin din mutum ba, dan kawai Username din ya banbanta da sunan dake a ID din mutum ba.
Yadda abun yake shine, idan mutum ya taka doka na Facebook, wanda ya haddasa rufe shafin, duk lokacin da kazo ɗaukaka ƙara ko neman dawo da shafin da aka rufe zasu bukaci ID ɗinka wanda yayi daidai da sunan dake jikin shafin din naka. Idan baiyi daidai ba shine yake zama matsala duk da haka sukan warware matsalar a yawancin lokuta.
A tsarin kamfanin Meta zaku iya amfani da sunan da kowa ya fi saninku dashi, ko ma sunan banza, ko sunan sana’a. Wannan tsarin nasu yananan a rubuce a Facebook Help Center.
Sakamakon bincike:
Binciken Alkalanci ya kasa samun wani waje da kamfanin Meta ya bayyana cewa ya ba ƴan Najeriya wa’adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa ba. Sannan babu wani labari dake nuna cewa akwai haɗin gwiwa tsakanin Meta da gwamnatin Najeriya. Sannan kuma babu inda Meta ya bayyana cewa yawan shafukan Facebook a Najeriya ya kai sama da miliyan 700. Bisa rashin samun sahihan bayanai daga a shafukan Meta da hukumomin gwamnatin Najeriya dangane da wannan iƙirarin yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ƙarya ne.
