Hukunci: Ƙarya ne
Bisa bayanan shugaban kasar Ghana John Mahama, ministan harkokin wajen Ghana da suka ce ƙasar bata da shirin maida ƴan Najeriya ƙasar su, sannan kuma an kasa samun labarin daga sahihan gidajen jaridu, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarya ne.
Akwai dai kiraye-kirayen da wasu ƴan ƙasar Ghana keyi na gani gwamnatin ƙasar ta maida ƴan Najeriya ƙasar tun bayan batun naɗin sarautar Sarki ƴan ƙabilar Igbo a ƙasar ta Ghana.
Wasu da dama sun ƴada tsoffin bidiyo, hotuna dama waɗanda aka haɗa ta amfani da ƙirƙirrarriyar basirar AI a matsayin zanga-zangar korar ƴan Najeriya.
Wasu ƴan ƙasar ta Ghana dai sunyi zanga-zangar korar ƴan Najeriya daga ƙasar su a ƙarshen watan Yuli.
Iƙirari:
Wani shafin Tiktok ya wallafa wani bidiyo da aka ga wani na iƙirarin cewa ƙasar Ghana ta amince a mayar da ƴan Najeriya ƙasarsu. ((https://vm.tiktok.com/ZSSa1RsBA/))
“Ghana nan har an zauna an yanke hukuncin babu mafita illa dawo da ƴan Najeriya, domin suka bari hakan ya cigaba da wanzuwa zamu mamaye musu ƙasar su.”
Bincike:
Duk da cewa a shekarun baya Ghana ta taɓa dawo da ƴan Najeriya, to amma wannan sabon kiraye-kirayen bai sanya gwamnatin ƙasar ko majalisar dokokin ƙasar amincewa da dawowa da ƴan Najeriya ba.
Shugaban kasar Ghana John Mahama ya tabbatarwa ‘yan Najeriya mazauna Ghana cewa babu batun maida su gida Najeriya.
Shugaba Mahama ya fadi hakan ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar Najeriya bisa jagorancin ministar kasa a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya inda suka je Birnin Accra domin tattaunawa da hukumomin Ghana.

A wata ganawa da ministan harkokin wajen Ghana da takwarar sa ministar ƙasa a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Bianca Ojukwu, gwamnatin Ghana ta tabbatar da cewa bata da shirin kora ko maida ƴan Najeriya.
Alkalanci ta tuntubi wani ɗan jaridar ƙasar Ghana
Kent Mensah inda ya bayyana cewa ƙarya ake yaɗawa kan cewa Ghana ta amince ta kori ƴan Najeriya, ya ƙara da cewa ko kiraye-kiraye da zanga-zangar da akayi mutane ƙalilan ne ke wannan buƙatar.
Haka zalika babu wata sahihiyar kafar yaɗa labarai data ruwaito cewa gwamnantin Ghana ta amince ta dawo da ƴan Najeriya.
Sakamakon bincike:
Bisa bayanan shugaban kasar Ghana John Mahama, ministan harkokin wajen Ghana da suka ce ƙasar bata da shirin maida ƴan Najeriya ƙasar su, sannan kuma an kasa samun labarin daga sahihan gidajen jaridu, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarya ne.
Kamaru ta bada umarnin kama ƴan Najeriya?
A bidiyon da aka wallafa a shafin TIKTOK din ya ƙa ra da cewa ƙasar Kamaru sun daɗe da bada umarnin kama ƴan Najeriya a ƙasar.
“Nan Kamaru tun kimanin shekara guda ma aka sanar da kamen ƴan Najeriya ana dawo dasu ƙasarsu. Kamaru ɗan Najeriya zai shiga ana sarautar da.”
Binciken kafar tantance labarai ta Alkalanci bai gano inda aka ruwaito cewa hukumomin ƙasar Kamaru sun bada umarnin farauta ko kama ƴan Najeriya dake zaune a ƙasar ba.
Ofishin jakadancin Najeriya a Douala Kamaru ya bayyana a shafinsa cewa akwai ƴan Najeriya akalla miliyan bakwai (7miliyan) a ƙasar Kamaru.
Sakamakon bincike:
Bisa rashin samun labarin cewa ƙasar Kamaru ta bada umarnin farautar da kuma kama ƴan Najeriya a ƙasar. Domin kuwa irin wannan labari yayi girman da manyan kafafen yaɗa labarai dole su rawaito kuma zai zama batun diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarya ne.
