Fayyace abubuwaShin gwamnatin jiha nada hurumin rufe gidan radiyo?

Shin gwamnatin jiha nada hurumin rufe gidan radiyo?

-

Gwamnan jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Najeriya ya  bayar da umarnin rufe tare kwace lasisin gidan radiyo mai suna Badeggi FM, saboda zargin Ingiza mutane su tada tarzoma wanda gidan radiyon ya musanta.

Wa zai iya rufe gidan radiyo?
Kundin tsarin mulkin Najeriya sashe na 39 ya baiwa ‘yan kasa damar mallaka tare da bude gidan jarida…
Dokar Najeriya dai ta baiwa hukumar kula da kafafen yada labarai NBC damar cin tara, soke lasisi tare da rufe kafar yada labarai Idan har an sami kafar da laifi bayan bincike.
Shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya Afam Osigwe ya ce “babu wanda doka ta bashi damar rufe gidan jarida ba tare da bin doka ba.”
Itama ma’aikatar yada labarai ta Najeriya a wata sanarwar manema labarai da mai baiwa ministan yada labarai shawar Rabi’u Ibrahim ya sanyawa hannu ta tabbatar da cewa hurumin rufe ko soke lasisin gidan jarida na karkashin hukumar kula da kafafen yada labarai ta Najeriya wato NBC ce kawai.
Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnatin jihar ta Neja da ta mika korafinta kan gidan jaridar ga hukumar NBC.
Sakamakon bincike:
Bisa bayanin kundun tsarin mulkin Najeriya, kungiyar lauyoyi ta kasa da kuma ma’aikatar yada labarai ta Najeriya suka tabbatar da cewa hurumin dakatar ko soke lasisin gidan jarida na hannun hukumar NBC ne ba wata hukuma ko gwamnatin jiha ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar