Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa Birtaniya ta yaɗu gidajen labarai ke bayyana cewa wannan irin ziyara ita ce ta farko da shugaban Najeriya zai kai tun shekarar 1989 wato shekaru 37 da suka wuce lokacin shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida.
Akwai mutane da dama dake ganin cewa an sha ganin shugabannin Najeriya sun kai ziyara zuwa Burtaniya amma yanzu ake cewa ita ce ta farko cikin shekaru 37.
Ga yadda abin yake, Alkalanci ta tuntuɓi ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya kan cewa tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa Yar’adua da matarsa Turai sun taɓa kai ziyarar aiki zuwa Burtaniya tare da ganawa da Sarauniyar Ingila da Firaministan wancan lokaci.
Haka zalika a shekarar 2018 tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari shima ya kai ziyarar aiki zuwa Burtaniya inda ya gana da Firaministar Burtaniya ta wancan Lokaci Theresa May.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntuɓi Ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya inda ofishin ya bayyanawa Alkalanci yadda abin yake.
Ofishin yace akwai banbanci tsakanin abinda ake kira official visit da kuma state visit.
Ziyarar aiki wato Official visit
Yayin da marigayi Umaru Musa Yar’adua da marigayi Buhari suka kasance sunyi official visit ne wanda iya tattauna wa da taruka ne na batun siyasa, diplomasiyya da tattalin arziki.
Ziyarar aiki ta musamman wato state visit
To amma idan aka zo maganar state visit wato ziyarar aiki ta musamman tana nufin cewa masarautar Ingila ce ta turo da wasiƙar gayyata ga shugaban Najeriya inda a ziyarar za a karrama shugaban ƙasar ta cin abinci na sarauta a Windsor Castle da kuma duba dakarun tsaron masarauta wato Royal Guards.
Tun bayan tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida dai babu shugaban ƙasar Najeriya da Masarautar Ingila ta turowa da wasiƙar gayyatar ziyarar aiki ta musamman.
Shugabannin Najeriya uku da suka taɓa samun irin wannan tarɓa a baya sune; Yakubu Gowon, marigayi Shehu Shagari da kuma Ibrahim Badamasi Babangida.
