BindiddigiZiyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na...

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

-

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa Birtaniya ta yaɗu gidajen labarai ke bayyana cewa wannan irin ziyara ita ce ta farko da shugaban Najeriya zai kai tun shekarar 1989 wato shekaru 37 da suka wuce lokacin shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida.
Akwai mutane da dama dake ganin cewa an sha ganin shugabannin Najeriya sun kai ziyara zuwa Burtaniya amma yanzu ake cewa ita ce ta farko cikin shekaru 37.
Ga yadda abin yake, Alkalanci ta tuntuɓi ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya kan cewa tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa Yar’adua da matarsa Turai sun taɓa kai ziyarar aiki zuwa Burtaniya tare da ganawa da Sarauniyar Ingila da Firaministan wancan lokaci.
Haka zalika a shekarar 2018 tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari shima ya kai ziyarar aiki zuwa Burtaniya inda ya gana da Firaministar Burtaniya ta wancan Lokaci Theresa May.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntuɓi Ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya inda ofishin ya bayyanawa Alkalanci yadda abin yake.
Ofishin yace akwai banbanci tsakanin abinda ake kira official visit da kuma state visit.
Ziyarar aiki wato Official visit
Yayin da marigayi Umaru Musa Yar’adua da marigayi Buhari suka kasance sunyi official visit ne wanda iya tattauna wa da taruka ne na batun siyasa, diplomasiyya da tattalin arziki.
Ziyarar aiki ta musamman wato state visit
To amma idan aka zo maganar state visit wato ziyarar aiki ta musamman tana nufin cewa masarautar Ingila ce ta turo da wasiƙar gayyata ga shugaban Najeriya inda a ziyarar za a karrama shugaban ƙasar ta cin abinci na sarauta a Windsor Castle da kuma duba dakarun tsaron masarauta wato Royal Guards.
Tun bayan tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida dai babu shugaban ƙasar Najeriya da Masarautar Ingila ta turowa da wasiƙar gayyatar ziyarar aiki ta musamman.
Shugabannin Najeriya uku da suka taɓa samun irin wannan tarɓa a baya sune; Yakubu Gowon, marigayi Shehu Shagari da kuma Ibrahim Badamasi Babangida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labarin kakkabo jirgin Iran a Sokoto?

Akwai iƙirari da wasu shafukan sada zumunta na Facebook kamar ALFIJIR NEWS da MEDIA ADVERTS da suka wallafa labarin...

Netanyahu na raye ko ya mutu?

Akwai dai iƙirarai da jita-jita da dama dake yaɗuwa a kafafen sada zumunta dake cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu...

Ina gaskiyar labarin cewa an fitar da shugaba Tinubu zuwa Faransa saboda cutar kansa?

Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna MEDIA ADVERTS ya wallafa wani labari dake iƙirarin cewa an fitar da shugaban Najeriya...

Labarin sanya Alkur’ani babban darasi cikin makarantun Senegal ƙarya ne

Labarin sanya Alkur'ani babban darasi cikin makarantun Senegal ƙarya ne Labaran da suka shafi addini kan kasance masu ɗaukar hankali...

Yadda Ake Ta Maimaita Labarin Ƙarya Kan Shugaba Putin Da Dokar Kare Mutuncin Alkur’ani

“Shugaban Rasha Putin ya saka dokar hukunci mai tsanani ga duk mutumin da aka kama shi yana ɓatanci ga...

Ko Birtaniya da Faransa na shirin baiwa Ukraine makamin nukiliya?

Yayin da yaƙin da Rasha ke gudanarwa Ukraine ya shiga shekara huɗu akwai iƙirarai kala-kala dangane da yaƙin. Iƙirari: Wani shafin...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labarin kakkabo jirgin Iran a Sokoto?

Akwai iƙirari da wasu shafukan sada zumunta na Facebook...

Netanyahu na raye ko ya mutu?

Akwai dai iƙirarai da jita-jita da dama dake yaɗuwa...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar