Hukunci: Ƙarya ne
Bidiyo da ake yadawa tsohon bidiyo ne yayin da gwamnan Borno da sauran mutane ke tarbar gawar Isa Gusau a shekarar 2024.
Akwai dai wani bidiyo dake yawo matuka a shafukan Tiktok da Facebook inda ake nuna cewa gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce aka dawo da ita Najeriya.
Wannan bidiyo na kuma cigaba da yaduwa a kafar tura sakonni ta WhatsApp.
Muhammadu Buhari ya rasu ranar lahadi a wani asibiti a Birnin Landan cikin wata sanarwa da Garba Shehu yayi a ranar.
Tuni dai tawagar gwamnatin Najeriya suka bisa shugabancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima suka isa Landan don dawowa da gawar zuwa Najeriya.
Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda yace a Daura za’a binne tsohon shugaban kasar.
To sai dai kafar tantance labarai tayi bincike kan wannan bidiyo dake yaduwa inda ta gano cewa tsohon bidiyo ne na shakarar 2024 inda gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da makarabban gwamnati ke karbar gawar marigayi Isa Gusau.
Sakamakon bincike:
Bisa gano cewa wannan bidiyo tsoho ne kuma bashi da alaka da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, sannan babu wani bidiyo sahihi da ya tabbatar da cewa tun ranar lahadi an dawo da gawar ta Buhari, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyo karya ne.
